Bayan da kasar Sin ta gabatar da rahoton yanayin gudanar tattalin arzikinta a watan Yuli a jiya Juma’a 15 ga watan nan, kungiyoyin kasa da kasa da dama sun nuna kyakkyawan fata ga makomar bunkasar tattalin arzikin kasar, suna masu hasashen samun karin nasarori bayan aiwatar da manufofin fadada bukatun cikin kasa, yayin da kasar Sin din za ta kara samun karfi da kuzarin raya tattalin arzikinta.
Bayan fitar da rahoton, ana gano cewa an tabbatar da bunkasar tattalin arzikin Sin yadda ya kamata. Alal misali, yawan jarin da aka zuba a kasar tun daga watan Janairu zuwa Yuli ya karu da kashi 1.6 cikin dari, yayin da alkaluman yawan sha’anin samar da hidimomi na kasar ya karu da kashi 5.9 cikin dari kan na makamancin lokacin bara. Alkaluman kididdigar dake shafar fannoni da dama a kasar Sin, sun nuna saurin karuwa, inda aka shaida cewa, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da karuwa yadda ya kamata.
Bisa yanayin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin a halin yanzu, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya daga hasashen saurin bunkasar tattalin arzikin Sin na shekarar 2025 zuwa kashi 4.8 cikin dari. Kazalika, a kwanakin baya, tawagar wakilan ‘yan kasuwa ta kasar Amurka ta kawo ziyara kasar Sin, wanda hakan ya shaidawa duniya cewa, kasuwar kasar Sin tana da muhimmanci. Haka zalika kuma, sassan kasa da kasa sun fi son zuba jari ga kasar Sin a shekarun baya-bayan nan, wanda ke nuna kungiyoyin kasa da kasa da dama suna hasashen samun kyakkyawar makomar bunkasar tattalin arzikin Sin. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp