A dai dai lokacin da ake ci gaba da zaman dar-dar a yankin gabas ta tsakiya sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Falasdinu da Isra’ila, masarautar Saudiyya ta kaddamar da wani sabon shiri da nufin kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Wannan sanarwar dai na zuwa ne bayan gazawar shekaru da dama da kasashen duniya suka yi na warware rikicin Isra’ila da Falasdinu, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dama yakin da ake gwabzawa a tsakanin yankunan biyu.
- Kashin Shettima Ya Dawo Nijeriya Bayan Taron Majalisar Ɗinkin Duniya Na 79
- Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Ya Ce Babu Rashin Fahimta Ko Shubuha Dangane Da Kuduri Mai Lamba 2758
Ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan ne ya gabatar da kungiyar hadin kan kasa da kasa don aiwatar da shirin ‘yantar da yankin Falasdinu a lokacin da yake jawabi a wani babban taro da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, OIC da Norway suka halarta.
Yarima Faisal ya bayyana cewa, shirin hadin gwiwa ne tsakanin kasashen Larabawa da na Turai, inda ya bayyana cewa, taron na farko na kungiyar zai gudana a birnin Riyadh.
Bugu da kari, Josep Borrell, babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar Tarayyar Turai, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da tarukan a biranen Riyadh da Brussels.
“Mun kuduri aniyar yin aiki don samar da ingantaccen tsari da ba za a iya juyawa ba don cimma daidaito da cikakken zaman lafiya,” in ji Yarima
Faisal, ya yi kira da a dauki matakin gama gari don cimma sakamako mai ma’ana, tare da mai da hankali kan tsagaita bude wuta nan take tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas da kuma kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.