An kama wani wanda ake zargi da taimaka wa wajen shigar da wani dan jarida da ba musulmi ba cikin birnin Makkah wanda hakan ya sabawa dokar haramta wa wadanda ba musulmi ba shiga birnin mai tsarki.
Jami’an Saudiyya sun sanar da hakan a ranar Juma’a cewa dan jaridar kasar Isra’ila, Gil Tamari, wanda ya je Saudiyya don bayar da rahotannin ziyarar da shugaban Amurka Joe Biden, ya kai a can, ya yi amfani da wannan damar ya shiga cikin birnin Makkah a boye, ya zagaya tare da daukar wani bangare na garin domin gidan talabijin na Channel 13 News.
- Akwai Kwanciyar Hankalin Yin Kasuwanci A Nijeriya — Lai Mohammed
- Tinubu Da Gwamnonin Kudu Ba Su Halarci Taron Da Buhari Ya Yi Game Da APC Ba
Haskawar da a ka yi a tashar talabijin din ya haifar da cece-kuce da kuma gargadin cewa zai iya lalata alakar da ke tsakanin Saudiyya da Isra’ila.
Saudi Arabiyya, cibiyar addinin Musulunci, ba ta amince da Isra’ila ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Makkah ya ce an kama wani dan kasar Saudiyya tare da mika shi ga masu gabatar da kara.
“Shi (dan kasar) ya yi jigilar dan jaridar da ba musulmi ba, wanda ke da shaidar zama dan kasar Amurka, zuwa cikin birnin kasar (Makkah) ta hanyar da aka tanada ga musulmi, wanda ya saba wa doka.
“Duk masu shigowa cikin masarautar dole ne su mutunta kuma su bi ka’idoji, musamman wadanda suka shafi wurare masu tsarki.
“Duk wani cin zarafi za a dauke shi a matsayin laifin da ba za a aminta da shi ba,” in ji jami’in ‘yan sandan.
Jami’in ya ce an kuma aika da karar dan jaridar “wanda ya aikata laifin” zuwa gaban kotu.