Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Saudiyya ta kara wa’adin saukar jirage ga maniyyatan Nijeriya daga 4 zuwa 6 ga watan Yuli, 2022.
A wani rahoto da BBC Hausa ta Nakalto, ta bayyana cewa, Mataimakiyar daraktan kula da harkokin yada labarai na hukumar alhazai ta kasa, Hajiya Fatima Usara ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a Abuja.
Ta kara da cewa kara wa’adin ya zama wajibi ne sakamakon yawan jiragen da aka soke tashinsu da kuma wadanda aka samu jinkiri wajen tashinsu
Usara ta kuma bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon wasu dalilai da suka hada da kasa samar wa maniyya kudin guzuri da wasu hukumomin alhazai na jihohi suka yi, da rashin wadatattun kudin biza, tare da gaza samun sakamakon gwajin Korona da aka yi wa maniyyatan a kan lokaci.