Masarautar Saudiyya ta nada Sheikh Dr. Saleh bin Humaid a matsayin sabon babban Muftin masarautar kuma shugaban majalisar malamai na kasar.
Humaid mai kula da Masallatan Harami biyu ne, Yarima Salman ne ya nada shi.
Zai gaji Sheikh Abdulaziz, wanda ya rasu ranar Talata yana da shekaru 82 a duniya.
A halin yanzu dai Humaid yana daya daga cikin Limamai tara na Masallacin Harami na Makkah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp