Ofishin jakadancin Saudiyya a Nijeriya reshen jihar Kano ya gabatar da taron raba dabino tan hamsin a gidan Gwamnatin Kano da wasu daga cikin jihohin Arewacin kasarnan.
A wani sako da aka rabawa manema labarai a jiya Juma’a a babban birnin tarayya Abuja, jakadan Saudiyya a Nijeriya, Khalil Admawy, ya tabbatar da ƙoƙarin ƙasar Saudiyya wajen gabatar da ayyukan jin kai a Nijeriya.
- Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya
- Noman Dabino: Jigawa Ta Yi Hadaka Da Saudiyya
Shirin yana cikin ayyukan jin kai na shekara-shekara da ƙasar Saudiyya take yi a karkashin Gidauniyar taimako ta Yarima Bin Salman.
Ginshiƙin taimakon shi ne tallafawa marasa ƙarfi da kuma bunƙasa tsohuwar dangantakar da ke tsakanin Nijeriya da Saudiyya.
Jakadan Saudiyya ya godewa Sarki Salman Bin Abdulaziz da Yarima Muhammad Bin Salman bisa kokarinsu na tallafawa musulmi a fadin duniya.
Ya kuma ƙara jidadda matsayar Saudiyya wajen hidimtawa addinin musulunci da bayar da taimako ga mabuƙata.
Banda tallafin dabino, Saudiyya ta kuma ƙudiri aniyar tallafawa mutane da kayan abinci lokacin shan ruwa, wanda za a yi a babban birnin tarayya Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp