Kasar Saudiyya ta yi watsi da duk wani yunkuri na kwashe Falsdinawa daga yankinsu kamar yadda shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana.
Saudiyya ta ce ba za ta kulla duk wata alaka ta diflomasiyya da Isra’ila ba tare da an bai wa Falsdinawa kasarsu mai ‘yanci ba.
- Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
- Farashin Kayan Abinici Ya Karu Da Kashi 91.6 Cikin Shekara Daya -NBS
Wani mai magana da yawun kungiyar Hamas ya bayyana shawarar ta Donald Trump a matsayin abin takaici, wadda za ta haifar da karin zaman tankiya a yankin.
Haka nan an samu wasu daga cikin sanatocin Amurka na jam’iyyar Democrats wadanda suka soki batun, inda daya daga cikinsu ya bayyana lamarin a matsayin “yunkurin kawar da wata kabila daga doron kasa.”
Tuni Masar da Jordan suka yi watsi da batun tayin karbar Falsdinawan.