• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Saurayi Ya Babbake Gawar Budurwarsa Bayan Dirka Mata Ciki A Bauchi

Ya Kashe Ta Sannan Ya Babbake Gawarta

by Khalid Idris Doya
3 years ago
Saurayi

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta samu nasarar cafke wani saurayi mai shekara 27 a duniya, Munkaila Ado bisa zargin kashe budurwarsa mai suna Safiya Danladi, ‘yar shekara 13 a duniya da ke kauyen Pali a karamar hukumar Alkaleri a cikin garin Bauchi. 

Bayanai sun nuna cewa kafin safiya ta mutu tana dauke da cikin watanni hudu wanda kuma shi saurayin nata ne ya mata.

  •  Sharhi: Siyasar Ubangida Da Zaben Shekarar 2023
  • Za A Dawo Da Shingen Binciken ‘Yansanda A Fadin Nijeriya

A sanarwar da kakakin ‘yansadan Bauchi, Ahmed Wakil ya fitar, ya ce Munkaila ya dauki Safiya zuwa jihar Gombe domin zubar da cikin da ya mata, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Daga baya kuma, Munkaila Ado ya yanke hukuncin kashe ta bayan rashin nasarar zubar da cikin da ya yi wa budurwar tasa.

Sanarwar ta ce, “Wanda ake zargi (Munkaila) ya bayyana da kansa cewa yarinyar da ta bace din budurwarsa ce da take dauke da cikin watanni hudu da sanin mahaifiyarta ya yi kokarin zubar da cikin, shi kuma mahaifinta Alhaji Danladi Mohammed ba shi da masaniya.”

LABARAI MASU NASABA

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

Sanarwar ta ci gaba da cewa “Munkaila ya hada baki da mahaifiyar yarinyar ‘yar shekara 13 da wani mai suna Muazu, inda suka dauki yarinyar zuwa Gombe da nufin zubar da cikin.

“Bayan da suka isa Gombe sun samu wata mata mai suna Hajiya Amina Abubakar mai shekara 50 da gidanta ke Jekada Fari da ke bayan asibitin Kwararru na Gombe, inda aka yi wa yarinyar wasu abubuwa da nufin zubar da cikin”.

Bayan rashin nasarar zubar da cikin, sanarwar ta kara da cewa a lokacin da suke hanyar dawowa Bauchi, Munkaila da Muazu suka shake Safiya har ta mutu.

Daga baya kuma suka kona gawarta sannan suka binne ta a wani rami.

‘Yansandan sun kara da cewa za su gurfanar da wadanda suka kama a gaban kotu bisa tuhumarsu da kisan kai gami da cin zarafi da keta haddin karamar yarinya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Manyan Labarai

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure
Manyan Labarai

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai
Manyan Labarai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Next Post
Kyamar ‘Yan Shaye-shaye Ke Kara Tsunduma Matasa Ayyukan Assha -Fatima Bature

Kyamar 'Yan Shaye-shaye Ke Kara Tsunduma Matasa Ayyukan Assha -Fatima Bature

LABARAI MASU NASABA

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.