Wani matashi mai shekaru 19 mai suna Mohammed Ibrahim, mazaunin Sabon-Layi da ke wajen birnin Bauchi a Jihar Bauchi, ya daba wa budurwarsa mai suna Emmanuella Ande wuka har lahira bayan wani rikici da ya barke a tsakaninsu kan kudi naira 5,000.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa kafin faruwar lamarin, Mohammed ya sace kusan Naira 400,000 na mahaifinsa domin ya kashe wa Emannuella, wadda ‘yar Jihar Filato ce, bayan sun shirya haduwa a Fatakwal a Jihar Ribas.
- Mahara Sun Sace Sarki Da Fadawansa A Garin Pupule Na Jihar Taraba
- Gwamnati Ta Shirya Fatattakar ‘Yan Bindiga A Duk Inda Suke – Ministan Tsaro
Mohammed wanda yanzu haka yana hannun ‘yansanda, ya hadu da marigayiyar ne a shafukan sada zumunta kafin daga bisani suka hadu a wani wurin shakatawa da ke unguwar Bayan-Gari a Bauchi.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, ya ce wanda ake tuhumar ya kuma daba wa wani Zaharadeen Adamu mai shekaru 36 wuka, wanda ya yi kokarin ceton Emmanuella.
“Wannan mummunan al’amari ya faru ne a lokacin da wadda aka kashe ta bukaci kudi naira 5000 yayin da ita budurwar ta nemi ya biya ta wasu da ta ke bin sa, hakan ne ya sa cacar-baki ta kaure har fads ya shiga tsakaninsu lamarin da ya yi sanadin da ya sa ta samu rauni wanda ya kai ga mutuwarta.
“Ya daba wa budurwarsa Emmanuella Ande ‘yar Jihar Filato, wuka a kusa da kirjinta, a lokacin ne budurwar ta yi kururuwa, mutanen da ke wajen suka yi yunkurin kai mata dauki, suka bude kofar da karfi, inda wanda ake zargin ya kuma daba wa daya daga cikinsu wuka.
“Tawagar ‘yansanda ta yi gaggawar kai dauki, inda suka dauki budurwar zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi, inda aka tabbatar da mutuwarta.
“Haka zalika, an kwantar da Zaharadeen kuma an yi masa magani a asibitin an kuma sallame shi, a halin yanzu ana bincike a kan lamarin,” in ji kakakin.
SP Wakil ya ce an samu wuka daga hannun Mohammed, inda ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu.