Rundunar ƴansandan Jihar Delta ta kama wani matashi mai shekaru 27 mai suna Kelvin Obakpororo, bisa zargin kashe budurwarsa mai suna Excellence, wadda ita ce mahaifiyar ƴaƴansa biyu.
Lamarin ya faru ne a garin Sapele tsakanin ranar 26 zuwa 27 ga watan Yuni, 2025, kuma ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a shafukan sada zumunta, inda jama’a ke neman a yi adalci.
- Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos
- Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau
Kakakin ƴansanda na jihar, SP Bright Edafe, ya tabbatar da kama wanda ake zargi ranar Lahadi a Asaba, yana mai cewa: “Za ku tuna da rahotannin da suka bazu kan mutuwar Excellence da saurayinta ya kashe, wanda kuma shi ne mahaifin ƴaƴanta biyu. Da farko ya gudu, amma yanzu yana hannunmu kuma za a gurfanar da shi gaban kotu nan ba da jimawa ba.”
A yayin da ake tsare da shi, Obakpororo ya amsa cewa shi ne ya kashe ta, yana mai cewa ya yi hakan ne yayin da ya ke cikin mayen kwayar tramadol. “Ta na yin hulɗa da maza don kuɗi. Duk lokacin da ta zo gidana, sai ta shirya ta fita wajen wasu mazan. Mun yi faɗa a ranar, ta ɗauko wuka, ni kuma na ɗauki guduma. Na daka mata a goshi sau uku, ta faɗi. Ban san za ta mutu ba. Na sha tramadol 200mg. Kuskure ne. Ina ba da hakuri.”
Ya kuma amsa cewa yana harkar damfara ta intanet, kuma ya nuna nadama kan kisan mahaifiyar ƴaƴansa.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp