Tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwan Kantin Kwari, Alhaji Sanusi Umar Ata ya bayyana cewa yunkurin sauya fasalin kudi kokari ne na haramta amfani da naira a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake yi wa LEADERSHIP Hausa jawabi kan shirin sauya launin kudaden kasar nan da Gwamnan Babban Bankin ya shelanta, sannan ya samun amincewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
- Mayar Da Martani: Koriya Ta Arewa Ta Harba Makamai Masu Linzami Da Dama
- Da Dumi-Dumi: Mutane Da Dama Sun Mutu, Wasu Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Legas
Ata ya ce babbar matsalar shugabannin kasar nan ita ce, yadda ba sa amfani da shawarwarin masana kafin zartar da wani hukunci, sannan shi gwamnan babban bankin ya tuna kafin shi wasu sun yi, wanda ya kamata a kai wa majalisar kasa kafin zantar da hukunci na karshe.
A cewasa, ta yaya ta ya za a hukunta sama da mutum miliyon 200 saboda laifin mutanen da ba su wuce dubu biyu ba, kuma ai Shugaba Buhari idan zai tuna ya taba irin wannan aiki a lokacin yana matsayin shugaban kasa na mulkin soja, mai sauyin kudin a wancan lokacin ya haifar.?
Alhaji Ata ya ci gaba da cewa daga lokacin da aka shelanta cewa daga ranar 15 ga watan nan za a fara amfani da sabbin kudaden, cikin kasa da awo 24 farashin dala ta koma sama da Naira dari takwas, kuma idan ba a sake shirin ba nan da wata daya Dala za ta iya kai Naira dubu a madadin dala daya.
Ya bukaci jama’a su yi karatun ta-na-tsu wajen zabar sabbin shugabanni a zaben 2023.