• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sauya Sheka Ya Sa APC Ta Samu Gagarumin Rinjaye A Majalisun Tarayya

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
4 months ago
APC

Yawan ficewa daga jam’iyyun adawa a majalisar tarayya ya karu, wanda ya sanya yawan ‘yan majalisar jam’iyyar APC mai mulki ya kai 68 a majalisar dattawa da kimanin 207 a majalisar wakilai, tun bayan kaddamar da majalisar tarayya ta 10 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Bisa yunkurin Sanata Neda Imasuen na Jam’iyyar LP, wanda ke wakiltar Edo ta kudu, wanda ya sanar da shigarsa cikin APC ranar Alhamis, 12 ga Yuni, ana sa ran jam’iyyar za ta kara karfi a majalisar dattawa daga kujeru 68 zuwa 69 idan an sanar da shigarsa a hukuma.

  • Bin Hanya Daya Da Aiwatar Da Matsayar Da Aka Cimma Muhimmin Mataki Ne Na Ba Da Tabbaci Ga Huldar Ciniki Da Tattalin Arzikin Sin Da Amurka
  • Gwamnati Ta Yi Karin Haske Kan Biyan Tallafin Rage Radadi Da Mafi Karancin Albashi

Adadin na iya karuwa zuwa 70 idan Sanata Ahmed Wadada Aliyu, wanda ke wakiltar mazabar Nasarawa ta yammaci, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar SDP, inda har ya dawo APC.

A cikin zauren majalisar dattawa, an samu ficewar sanatoci guda uku daga Kebbi, inda suka sauya sheka PDP zuwa APC, wanda ya rage karfin PDP daga kujeru 36 zuwa 30. A cikin majalisar wakilai kuwa, yawan PDP ma ya ragu sosai.

A farkon kaddamar majalisar dattawa ta 10, APC ta kasance tana da kujeru 59; PDP na da 36; LP na da 8; SDP na da 2; NNPP na da 2; APGA na da 1; da kuma YPP na da guda 1.

LABARAI MASU NASABA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan PDP guda biyu da ‘yan majalisar wakilai guda bakwai daga PDP.

Tun da aka rantsar da majalisar dattawa ta 10 a watan Yuni 2023, ‘yan majalisa da dama sun koma APC, wanda ya sa jam’yyar na ci gaba da samun gagarumar rinjaye.

Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba, mai wakiltar Sakkwato ta kudu na jam’iyyar PDP, ya koma APC a watan Maris 2024. Da farko, Sanata Ifeanyi Ubah ya canza sheka daga YPP zuwa APC a watan Oktoba 2023 kafin rasuwarsa.

A watan Fabrairu na 2025, Sanata Ned Munir Nwoko, mai wakiltar Delta ta arewa ya bar PDP ya koma APC, yana mai bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida a PDP na Delta ya sa ya sauya sheka.

Haka kuma, Sanata Ezenwa Onyewuchi, mai wakiltar Imo ta gabas, wanda aka zaba a karkashin jam’iyyar LP, ya koma APC a watan Yulin 2024, yana mai cewa batutuwan cikin gida ne suka jawo hakan.

Sanata Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta kudu, wanda aka zabe a karkashin tutun jam’iyyar NNPP, ya sauya sheka zuwa APC a ranar 7 ga Mayu, 2025.

Bayan haka, sanatoci guda uku daga Kebbi da suka hada da Adamu Aliero, mai wakiltar Kebbi ta tsakiyar da Yahaya Abdullahi, mai wakiltar Kebbi ta arewa, da Garba Maidoki, mai wakiltar Kebbi ta kudu, suka sauya sheka daga PDP zuwa APC bayan taron da Shugaban kasa Bola Tinubu ya kira a fadar shugaban kasa.

Kazalika, tun lokacin da aka kaddamar da majalisar wakilai ta 10 a watan Yuni na shekarar 2023, wannan majalisa ya fuskanci lamarin sauya sheka ga wasu daga cikin ‘yan majalisa, wanda ya faru sakamakon sabani na ciki gida a jam’iyyu, matsin lamba na mazabu da kuma sabbin tsarin siyasa wanda hakan ya amfanar da APC.

Da farko, APC ta rike kujeru 175; PDP na da 118; LP na da 35; NNPP na da 19; APGA na da 5; ADC na da 2; SDP na da 2; YPP na da 1; yayin da kujeru uku babu kowa. Gaba daya dai, ‘yan adawar na rike da kujeru 182 fiye da APC. Amma yau, adadin kujerun ’yan adawar ya ragu zuwa 150.

An fara wannan salo ne a ranar 23 ga Yuli, 2024, lokacin da Hon. Idris Salman, mai wakiltar Kabba-Bunu/Ijumu a Jihar Kogi, ya canza sheka daga ADC zuwa APC, yana mai cewa akwai rikicin shugabanci da kuma matsi daga mazabarsa wanda ya sa ya koma jam’iyyar da ke mulki.

A watan Oktoba na 2024, Hon. Chris Nkwonta, mai wakiltar mazabar Ukwa ta yamma da Abiya ta yamma, ya bar PDP ya koma APC a ranar 2 ga Oktoba. Bayan haka a wannan watan, Hon. Sulaiman Abubakar, mai wakitar Gummi/Bukkuyum a Zamfara, shi ma ya fice daga PDP.

Jam’iyyar LP, wacce ta sami karfi a shekara ta 2023, ta fara fuskantar manyan tangarda a karshen shekarar.

A ranar 5 ga Disamba, 2024, ‘yan majalisar LP hudu cikin har da Hon. Chinedu Okere, mai wakiltar Owerri da kewaye da Hon. Mathew Donatus, mai wakiltar Kaura a Kaduna da Hon. Bassey Akiba, mai wakiltar Kalabar da kewaye /Odukpani a Kuros Ribas da Hon. Esosa Iyawe, mai wakiltar Oredo a Jijar Edo, sun koma APC, suna mai bayar da hujja kan rikice-rikicen cikin gida da suka kawo cikas ga kwazonsu.

Hon. Alfred Ajang, mai wakiltar Jos ta kudi / gabas a Filato, ya biyo bayansu a ranar 12 ga Disamba, yana jaddada dalilai masu kama da juna.

Sauyin ya ci gaba har zuwa 2025. A ranar 11 ga watan Fabrairu, Hon. Amos Magaji, mai wakiltar Zangon Kataf/Jaba a Jihar Kaduna) ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, yana mai cewa akwai rigima a cikin jam’iyyarsa ta asali.

Washagarin ranar, Hon. Garba Koko, wai wakiltar Kebbi shi ma ya shiga APC daga PDP.

A ranar 18 ga Maris, Hon. Jallo Hussaini Mohammed, mai wakiltar Igabi a Jihar Kaduna, da Hon. Adamu Tanko, mai wakiltar Gurara/Suleja/Tafa a Neja, sun sauya sheka zuwa APC daga PDP, su yi ikirarin cewa rashin jin dadin shugabancin PDP da kuma bayyana kwarin gwiwa a gwamnatin Tinubu su ne makasudin sauya shekarsu.

A ranar 27 ga Maris, Farfesa Chinwe Clara Nnabuife, mai wakiltar Orumba ta arewa/kudu, a Jihar Anambra) ta fice daga YPP zuwa APGA, tana zargin an tsame ta daga ayyukan jam’iyyar.

A watan Mayu na shekara ta 2025, ya zama lokacin da aka sami manyan sauye-sauye. A ranar 6 ga Mayu, ‘yan majalisar PDP guda shida daga Jihar Delta sun canza sheka zuwa APC bayan gwamnan jihar, Sheriff Oborebwori ya jagoranci wannan sauyin. ‘Yan majalisar dai su ne, Hon. Bictor Nwokolo, mai wakiltar Ika arewa, gabas/Ika ta kudu da Hon. Julius Pondi, mai wakiltar Burutu da Hon. Thomas Ereyitomi, mai wakiltar mazabar Warri da Hon. Nicholas Mutu, mai wakiltar Bomadi/Patani) da Hon. Ukodhiko Jonathan, mai wakiltar mazabar Isoko da Hon. Ezechi Nnamdi, mai wakiltar Ndokwa/Ukwuani).

A ranar 15 ga watan Mayu, ‘yan majalisa biyu daga jam’iyyar NNPP, Kabiru Usman da Abdullahi Sani, sun shiga APC. A wannan ranar, dan majalisan PDP mai wakiltar Oriade/Obokun daga Jihar Osun, Oluwole Oke, shi ma ya koma APC.

A ranar 22 ga Mayu, Hon. Sunday Umeha, mai wakitar Udi/Ezeagu daga Jihar Inugu, wanda aka zaba a karkashin LP, ya koma APC, yana cewa har yanzu matsalolin cikin gida na ci gaba da raba kawunan ‘ya’yan jam’iyyar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta
Tambarin Dimokuradiyya

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
peter
Tambarin Dimokuradiyya

Peter Obi Ya Bukaci INEC Ta Tabbatar Da Shaidar Karatun Dan Takara Kafin Shiga Zabe

October 10, 2025
Next Post
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin Fadar Shugaban Kasa Da Peter Obi Kan Tallafin Mai

LABARAI MASU NASABA

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

Xinjiang Ta Janyo Karin Jari A Rubu’i Uku Na Farkon Shekarar Nan

October 19, 2025
Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

Yadda Shagwaɓa Kananan Yara Da Kudi Ke Shafar Tarbiyyarsu

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.