Hedikwatar kotun daukaka kara da ke Abuja, ta bayyana cewa, sauya wa alkalai 21 wurin aiki a fadin kasar nan ba shi da dangantaka da hukuncin da kotu ta yanke na sakin wadanda ake zargi da ta’addanci a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu mai fafutukar kafa kasar Biyafira.
Ba kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana ba, kotun daukaka kara ta ce, sauyawa alkalan 21 daga cikin 81 wani abu ne da aka saba yi domin alkalan su samu kara tabbatar da adalci.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Tsohon Sakataren Gwamnatin Enugu Da Wasu
- Jam’iyyar PDP A Kebbi Ta Shirya Tarbar Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar
Babban rajistaran kotun, Malam Umar Mohammed Bangari, ya bayyana cewa, labaran da wasu kafofin yada labarai suka bayar na cewa alkalai guda uku da suka yanke hukunci ranar 13, ga watan Okotoba cewa a saki Kanu daga inda ake tsare da shi duk kansu an sauya musu wajen aiki.
Sannan ya ci gaba da cewa, a kashin kansa na babban Rajistara ya ce, alkali daya ne kawai daga cikin alkalai uku da suka yi shari’ar Kanu aka rage masa matsayinsa.
Kamar yadda bayanin ya nuna “An ankarar da kotun daukaka karar kan wani labara da aka buga a jaridar ranar Litinin 24, ga watan Okotoba 2022 mai kanun “Nnamdi Kanu: Alkalai 3 na kotun daukaka kara an sauya musu wajen aiki.”
“A gaskiya, sauya wa alkalai wurin aiki ba sabon abu ba ne, ana yin haka ne domin su kara samun kwarewa”.
Alkalai 21 daga cikin 81wadanda kuma suka hada da wasu alkalan guda 6 wadanda aka sauya wa wajen aiki.
Saboda haka ba gaskiya ba ne a ce, alkalan da suka yi shari’ar Nnamdi Kanu ne suka sa aka sauya wa wasu alkalai wajen aiki ba.
A karshe, muke kira ga wadanda sauyin wurin aikin ya shafa, su ci gaba da rungumar aikinsu da gudanar da shi cikin walwala da kwanciyar hankali, domin tabbatar da adalci ga wadanda suka gurfana a gabansu kamar yadda suka saba.