INJINIYA UMARA MUSTAPHA GONERI, shi ne, Babban Manajan Hukumar raya yankunan karkara da wutar lantarki (REB) ta jihar Yobe. A tattaunawar shi da wakilinmu ta jihar Yobe, MUHAMMAD MAITELA ya yi da shi, ya bayyana yadda gwamnatin jihar Yobe, karkashin Hon. Mai Mala Buni take kokari wajen bunkasa wutar lantarki a manyan garuruwa da karkara na jihar. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:
Wadanne hanyoyi ne Hukumar raya yankunan karkara da wutar lantarki take gudanar da ayyukanta?
Alhamdu lillahi, hukuma ce wadda take aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, amma bisa canzawar al’amurra yanzu ayyukanmu ba su tsaya a yankunan karkara kadai ba, hadda birane a karkashin tsarin da muke kira “Serbe and under serbed” ma’ana shi ne, akwai wasu ayyukan sanya wutar lantarki a wasu manyan garuruwa, amma saboda fadadar yawan gine-gine ya jawo karin bukatar isar musu da wutar lantarki. Sannan da kuma wuraren da an riga an ja musu wutar lantarki amma ta yi musu kadan saboda yawan jama’a.
Bugu da kari kuma, akwai garuruwa ko wuraren da ba a taba kai musu wutar lantarki ba, musamman kamar yankunan karkara. Baya ga haka kuma akwai asibitocin da muke dasu a fadin wannan jihar, wadanda suna bukatar wutar lantarki dare da rana, wanda zai taimaka wajen gudanar da aikace-aikacen kula da majinyata.
Bayan hasken wutar a asibitocin,ga samar da ruwa, a samu damar ajiye magunguna na musamman tare da gwaje-gwaje da aune-aune da sauran ayyukan da ba zasu yi ba sai da wutar lantarki a asibitocin mu.
Masu bibiyarmu za su so su ji yankunan da kuka sada da wutar lantarki kawowa yanzu?
Alhamdu lillah, zuwan gwamnatin Mai Mala Buni a karagar mulki, ya taka muhimmiyar rawa wajen bai wa wannan hukuma tamu cikakken goyon baya, musamman saboda yadda ayyukan mu suka shafi rayuwar talaka kai-tsaye. Wanda da kansa ya kiramu tare da bamu umurnin cewa mu shiga kowane lungu da sako domin mu kai ci gaba a kauyukan da ya dace a ce sun more romon dimukuradiyya.
Wanda hakan ya jawo mun nade kafar wandunanmu don aiwatar da umurnin gwamna, wanda a wannan zaman tattaunawa ba zai yuwu na lissafa maka adadin ayyukan da muka aiwatar ba; saboda zai kaimu gobe muna yi. Amma duk da haka, a takaice mun gudanar da aikace-aikacen sa wa da fadada wutar lantarki a manyan garuruwan jihar Yobe, wadanda suka hada da Damaturu, Buni-Yadi, Gashu’a, Nguru, Geidam da Potiskum. Ayyukan mu a wadannan manyan garuruwan su ne kai wutar a unguwannin da sun samu karuwar jama’a tare da bukatar wutar.
Sannan kuma inda suke da wutar lantarki, wanda daga baya sun fuskanci matsaloli ddaban-daban na na’urorin rarraba wutar lantarki (Transformer) ko turakun jawo wutar lantarkin, wanda ko a wannan makon kadai, taransifoma hudu muka raba a unguwannin Mazagani, Unguwan Jangam a Gadaka, Unguwar Tanda a Potiskum, dayan kuma a Unguwan Jaji a Potiskum. Wannan fa a cikin mako daya tal muka gudanar da wannan aikin, to ina ga ayyukan mu na shekara uku da rabi, wanda idan muka ce zamu lissafo su aiki ne ba karami ba.
Sai kuma kauyukan da muka jawa layukan wutar lantarki, wadanda ba a taba kai musu wutar ba a nan jihar Yobe; kauyukan da sun kai sama da 30- akwai kauyen Sumsum, kauyen Kasaisa, kauyen Mallam Adamu, kauyen Mirwa, da kauyen Zubak da su Lawan Kalam, da makamantan su; suna nan birjik. Wanda a takaice hukumar raya yankunan karkara da wutar lantarki a jihar Yobe, ta gudanar da ayyuka sama da 100 cikin shekara uku.
Wane yunkuri hukumar ku ke yi wajen ganin ta rage yawan matsalolin dauke wutar lantarki a jihar Yobe?
Mun gode Allah, kan wannan matsalar muna da kwararru da suke aiki wur-jan-jan wajen duba irin wadannan matsalolin, kuma da muka duba wannan matsalar, na daya ma mun hana amfani da falwaya na katako; sannan wasu unguwannin ba basu da wuta bane, tsarnu ne ba ma dakwalen katako ba kuma sai mutum ya sa wayar alminiyan farin nan, wanda nauyin wutarsa ya kai 70, amma ya ja da waya mai karfin wuta 35 na gaba dashi ya ja da waya mai karfin 16, wani kuma da irin wayar wutan nan siriri, baki da fari, duk irin wadannan su ke kawo matsala. Shi ne da muka kula da wadannan, duk unguwan da muka shiga sai mu ciresu mu watsar, muyi sabon zubi da wayoyi sabbi wadanda karfinsu ya kama daga 70 zuwa sama.
Sannan akwai wasu unguwanni, musamman a Damaturu, wadanda aka sanya wutar lantarki a da can, ko in ce an yi ayyukan cikin gaggawa a lokacin da aka samu sabuwar jiha. Kamar wurare ddaban-daban na ma’aikatu da rukunan gidaje irin su; 3-Bedroom na hanyar Potiskum, da Gashu’a, Ali Marami, Sani Daura Ahmed, da makamantan su, daga baya muka yi nazarin canza su baki daya, muka sanya sabbin falwaya. Haka abin yake a wasu manyan garuruwa; irin su Nguru, Yadin-Buni, Geidam.
A lokaci daya kuma, hukumarmu tana hada kai da Hukumar Samar da Wutar Lantarki (NEPA) ga kasa, saboda mun lura karfinsu ba sosai ba, bayan da aka mayar dasu kamfani wanda yasa gwamnatin jihar Yobe ta mayar da hankali sosai tare da daukar matakai wajen ganin al’ummar jihar basu shiga cikin matsalar wutar lantarki ba. Kuma sau da dama ana samun matsalar wutar ne idan nauyi ya yiwa taransifoma yawa, wanda idan mun gano haka sai mu raba unguwar gida biyu; sai mu kawo wani sabon taransifoma. Amma idan hanyoyin wutar ne ba kyau sai mu dauki matakan gano inda matsala take don magancewa. Sannan kuma muna bai wa mutane da ma’aikatu shawara duk lokacin da za su saka kayan wuta, su saka masu inganci domin kauce wa faruwar dukan wasu matsalolin dauke wutar.
Al’umma suna kukan yawan dauke wutar lantarki, wane mataki aka samu don samun wajen kyautatuwar lamarin a jihar Yobe?
Ko shakka babu akwai gagarumar nasara da muka samu a wannan fannin, sannan a da muna da layin wutar lantarki mai nauyin 132kb a Potiskum, wanda ya rarraba wutar zuwa sauran sassa. Inda daga baya aka samar da wani babban tasha mai karfin 330kb a Damaturu, wanda hakan ya raba jihar Yobe bangarori biyu- ta hanyar Potiskum shi ne zai je Nangere, Jakusko har Gashu’a zuwa Yusufari ya dawo Fika har zuwa Kukar-Gadu, shi kuma na Damaturu shi ne ya dauka zuwa Gulani, Yadin-Buni, ya nausa Babbangida, Dapchi, Yunusari, da Geidam.
Bayan wannan tsarin, gwamnatin jihar Yobe ta yi wani tsari na musamman wanda zai sanya ido wajen tabbacin wutar ya kai duk inda ake so, shi ne akwai wasu layukan raba wutar lantarki wanda ake kira 33kb, wanda sune suke daukar wutar zuwa manyan garuruwa, kuma dukanin layukan sabbi muka saka. Sannan mun saka ido duk inda aka samu wata matsala daga Damaturu zuwa Potiskum, daga Potiskum zuwa Gashu’a, haka daga Damaturu zuwa Dapchi zuwa Mayamari komai kankantar matsalar nan take zamu dauki matakin gyara. Sannan ma’aikatanmu kullum suna bibiyar duk inda suka hango wata matsala ba za ta yi sati ba sai an gyarata, a duk fadin jihar Yobe.
Wannan matakan ne suka jawo kaga ana samun wutar lantarki kowane lokaci a fadin jihar Yobe, musamman manyan garuruwan mu.
Ganin wannan hukuma tana karkashin Ma’aikatar Sufuri da Makamashi, ko akwai matsalolin da kuke fuskanta?
Abu na farko shi ne, tun kirkiro wannan hukuma ta raya yankunan karkara da wutar lantarki (REB) bata taba zaman kanta ba; kowane lokaci a karkashin Ma’aikata take. Ka ga kenan mun saba gudanar da ayyukanmu wuri guda, kuma muna aiki a matsayin uwa da ‘ya, sannan bamu kadai ne a karkashinta ba akwai Yobe Line, YOROTA ga Cargo International Airport. Dukan nasarorin da muke samu goyon baya ne daga wajensu, wanda gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni yake kai wa duk inda ya nufa.
Bugu da kari kuma, bisa wannan cikakken goyon baya da muke samu daga wajen Mai Girma Gwamna, wannan hukuma ita take kula da ayyukan samar da wutar lantarki a dukanin asibitocin mu a jihar Yobe. Wanda sun hada da Asibitin Koyarwa ta Jami’ar jihar Yobe, Asibitin Kwararru, Asibitin kula da lafiyar mata ta General Sani Abatcha, tare da asibitocin kwararru dake Potiskum, Gashu’a da Geidam, ka ga wadannan manyan asibitoci ne wanda Jama’a ke amfani dasu, kuma gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ya sanyasu a karkashin wannan hukuma tamu tare da bamu umurnin cewa duk yadda za a yi kar mu bari a rasa wutar lantarki a cikinsu.
Kuma yau shekara uku da rabi na wannan gwamnati mutum bai taba zuwa wadannan asibitocin, ko dare ko rana, ya rasa wuta ta kimanin minti biyar a cikinsu ba. Sai dai canji amma ba a rasa wuta ba.
Me za ka ce akan gudummawar gwamnatin jihar Yobe a wannan hukuma taku?
Haka ne, ko shakka babu idan ka ga yaro ya samu nasara a aikin sa, ai ya samu daurin gindin babba ne. Saboda haka kowane lokaci yana bamu cikakken goyon baya domin ganin wannan hukuma ta gudanar da ayyukanta cikin nasara. Ko shakka babu, Gwamna Mai Mala Buni, ya cika gwarzo mai kishin al’ummar jihar Yobe, wanda bisa wannan ya damka Hukumar a hannun hazikin Kwamishina, a Ma’aikatar Sufuri da Makamashi, wanda ya san aiki kuma amintaccen mutum wanda ya san makamar aiki, Honarabul Abdullahi Usman Kukuwa.
Haka kuma, Ma’aikatar Sufuri da Makamashi ta na bamu cikakken hadin gwiwan da ya dace domin samun nasarorin da muke samu.