Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta ce sayayyar kayayyakin amfanin gida a kasar Sin, karkashin tsarin nan na samar da rangwamen gwamnati, ta musayar tsofaffi da sabbin kayayyaki, ta bunkasa a shekarar 2024 da ta gabata.
Bayanai daga ma’aikatar sun nuna yadda sama da masu sayayya miliyan 37, suka amfana daga rangwamen da gwamnati ta samarwa ‘yan kasar ta Sin karkashin wannan tsari.
- Tinubu Ya Himmatu Wajen Kammala Titin Abuja Zuwa Kano Cikin Watanni 14 – Minista
- Zargin Kwacen Waya: Fusatattun Matasa Sun Bankawa Keken Adaidaita Sahu Wuta A Kano
Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin, sun nuna darajar kayayyakin amfanin gida, da kayan sauti da na kallo da aka sayar karkashin tsarin, ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 1.03, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 143.29 a shekarar ta bara. Wannan ne dai karon farko da darajar kudaden sayayyar wannan rukuni na kayayyaki ya haura yuan tiriliyan 1, adadin da ya shaida karuwar kaso 12.3 bisa dari a shekara guda.
Domin ingiza sha’awar sayayya, da bunkasa tattalin arzikin kasa, a watan Maris na shekarar bara, kasar Sin ta sanar da fara aiwatar da babbar manufar sauya kayayyakin da ake amfani da su a gidejen jama’a da sabbin samfura, ta hanyar mika tsofaffi, da yin cikon kudi mai rangwame, kusan shekaru 15 da aiwatar da makamanciyar wannan manufa.
A bangaren ingiza matakan cimma nasarar shirin, kasar Sin ta yanke shawarar fadada kayayyakin amfani a gidaje da za su ci gajiyar rangwamen sayayya da gwamnati ta tanada, daga abubuwa 8 a 2024 zuwa 12 a 2025, inda aka shigar da na’urar dumama abinci ta “microwaves”, da ta tsaftace ruwa, da na’urar wanke-wanke, da ta dafa shinkafa cikin tsarin. (Saminu Alhassan)