Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) na ƙasa, Alhaji Shehu Musa Gabam, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ba ta yi wa kowa alƙawarin samun tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ba.
Ya ce SDP ba za ta zama wata hanya da wasu manyan ‘yan siyasa za su bi don cimma burinsu na takara ba.
- INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye
- Kamfanin Apple Ya Sanar Da Zuba Sabon Jari A Fannin Samar Da Makamashi Mai Tsafta A Sin
A cewarsa, jam’iyyar na fuskantar kwarara sakamakon sauya sheƙar wasu manyan ‘yan siyasa zuwa cikinta, amma hakan ba yana nufin cewa za a bai wa wani daga cikinsu tikitin takarar shugaban ƙasa kai-tsaye ba.
“Babu Haɗin Gwiwa da Kowanne Ɗan Siyasa”
Alhaji Gabam ya jaddada cewa SDP ba ta yi wata yarjejeniya ko haɗin gwiwa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ko tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ko wani ɗan siyasa da ke neman tikitin takara a zaɓen 2027.
“Ba mu yi wa kowa alƙawarin takara ba, kuma ba mu da wata yarjejeniya da kowanne ɗan siyasa.
“SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi.
“Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a”
Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba.
“Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam.
SDP Na Ci Gaba da Ƙarfafa Tsarukanta
Ya ce jam’iyyar na shirin fitar da manufofi masu amfani ga al’umma, inda za ta ba da dama ga matasa da mata wajen shiga siyasa da kuma samar da sabbin shugabanni masu nagarta.
Wannan furuci na shugabannin SDP na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa wasu manyan ‘yan siyasa na shirin shiga jam’iyyar don samun damar takarar shugaban ƙasa.
Duk da haka, jam’iyyar ta bayyana cewa ba za ta sauya tsarinta domin kowanne mutum ba, kuma za ta bi ƙa’ida wajen fitar da ‘yan takara a zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp