Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bayan korarsa da jam’iyyar SDP ta yi tare da ƙaƙaba masa haramcin alaƙanta kansa da jam’iyyar na shekaru 30, inda mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan Harkokin watsa labari, Bayo Onanuga, ya kira shi da “Ɗan Gudun Hijirar Siyasa.”
Onanuga ya wallafa wannan shaguɓen a kafafen sada zumunta a ranar Litinin, yana mai bayyana abin da ke faruwa da El-Rufai a matsayin wani sabon ruɗanin siyasa da ya shiga tun bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa SDP.
- SDP Ta Kori Tsohon Gwamnan Kaduna El-Rufai
- Rikici Ya Turnuke Jam’iyyar SDP A Yayin Da Aka Samu Shugabanni Bangare Biyu A Kogi
Tun da farko, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar SDP na Ƙasa (NWC) ya sanar da korar El-Rufai daga jam’iyyar bisa zargin yin ƙarya da kuma nuna kansa a matsayin mamba alhali bai bi matakan yin rajista da tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba.
A cewar Kakakin Jam’iyyar na Ƙasa, Araba Rufus Aiyenigba, El-Rufai ya rika bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyyar SDP, duk da cewa shugabannin jam’iyyar a Jihar Kaduna sun sha bayyana cewa bai yi rajista ba.
An ce El-Rufai bai rajista a matakin mazaɓarsa ba, wanda shi ne matakin farko da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada kafin a karɓi wani a matsayin mamba.
Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane.
Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp