Gwamnatin jihar Katsina ta fara rabon buhunan siminti da fale-falen rufi (zinc) wanda kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) ta kaddamar da rabon tallafin ne a babban birnin jihar a ranar Alhamis ga mutane 611 da abin ya shafa a fadin kananan hukumomi 7 na jihar.
Da take jawabi a wajen taron, babbar daraktar hukumar ta SEMA, Hajiya Binta Dangani, ta ce bayar da kayayyakin gine-ginen na daga cikin alkawarin da gwamnan jihar Umar Dikko Radda ya yi na taimaka wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Ta ce, gwamna ne ya bayar da umarnin raba kayayyakin ga wadanda lamarin ya shafa, inda ta ce kasa da kwanaki 100 da gwamnatin Radda ta yi akan karagar mulki, ta kashe kusan Naira Miliyan 50 wajen samar da kayayyakin agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.