Kungiyar da ke sa ido kan yadda ake sarrafa dukiyar Jama’a ta maka gwamnonin jihohin kudancin Nijeriya a kotu kan zarginsu da kin bayyana yadda suka kashe naira biliyan 625 na tallafin mai da gwamnatin tarayya ta baiwa jihohin Abia, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Edo, Ribas, Ondo, Imo da Kuros Ribas a kwanan baya.Â
Lauyoyin kungiyar, Kolawole Daluwadare M Valentina Adegoke ne suka shigar da karar a madadin SERAP a makon da ya gabata a gaban babbar kutun da ke Abuja, wacce ke dauke da lamba FHC/ABJ/CS/2371/202.
Ta bukaci kotun da ta umarci gwamnonin da su wallafa cikakakkun bayanai akan yadda suka kashe wadannan kudaden tallafin man da gwamnatin tarayya ta ba su.
Daga cikin kudaden, an baiwa Jihohin Abia naira biliyan 4.8, Akwa-Ibom naira biliyan 128; Bayelsa naira biliyan 92.2, Kuros Ribas naira biliyan 1.3; Delta naira biliyan 110; Edo naira biliyan 3; Imo naira biliyan 5.5; Ondo naira biliyan 19.4 da Ribas naira biliyan 103.6.