Shafin yanar gizon sabuwar jam’iyyar adawa ta ADC ya tsaya sau uku cikin awanni 48 a sakamakon tururuwar da ƴan Nijeriya suke domin ganin sun shiga jam’iyyar tare kuma da neman bayanai a kan jam’iyyar.
Lamarin ya faru ne bayan da haɗakar ƴan adawa irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, suka amince da jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za su ƙalubalanci gwamnatin shugaba, Bola Tinubu a zaɓen shekara ta 2027.
- ‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027
- Ba A Taɓa Nuno Bidiyon Shugaban Jam’iyyarmu Ta ADC Yana Cusa Dala A Aljihu Ba —Dalung
An dai ƙaddamar da haɗakar ne a ranar uku ga watan Yuli a babban birnin tarayya Abuja, kuma tsayawar da shafin internet din ya yi ya nuna yadda ƴan Nijeriya suke buƙatar canji, kamar yadda masu sharhi a kan al’amuran siyasa suke ci gaba da bayyanawa.
Mai taimakawa Alhaji Atiku Abubakar a kafafen yada labarai na zamani, Demola Olarewaju, ya bayyana irin halin da shafin internet na jam’iyyar ya shiga.
“Sau uku shafin yanar gizon jam’iyyar ADC yana tsayawa cak tun daga lokacin da aka ƙaddamar da jam’iyyar saboda da yawan ƴan Nijeriya suna buƙatar wata jam’iyyar wadda ba APC ba, kuma tuni tana samun karɓuwa ” kamar yadda ya rubuta a shafisa na X.
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar.
Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci.
Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar canji.
Magoya bayan Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi suna ci gaba da nuna farin cikinsu da abin da ke faruwa a yanzu. Sai dai shugabannin haɗakar sun ce dole ne a ci gaba kula da lissafa abubuwan da ka iya faruwa a nan gaba kuma sai an yi haƙuri domin samun nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp