• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shagalin Murnar Bikin Bazara Ya Gabatar Da Shirye-shirye Masu Ban Sha’awa Ga Sinawa A Duk Duniya

byCMG Hausa
3 years ago
Bikin bazara

A yau Asabar jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da karfe 8:00 na daren, aka soma nuna shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar wato CMG ya gabatar ga Sinawa dake wurare daban daban na duniya.

Kundin abubuwan da suka yi fice a duniya na Guinness World Records ya amince da wannan shirin talabijin a matsayin “Shagalin talabijin da aka fi kallo a duniya”, tun daga shekarar 1983, wanda akan gabatar da shi a kowanne jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin kamar yadda aka tsara har tsawon shekaru 40.

  • Shugaban Nijeriya Ya Taya Sinawa Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Zomo

A shekarar 1983 ne, gidan talabijin na kasar Sin wato CCTV, ya watsa shagalin murnar shiga sabuwar shekara na farko na bikin bazara kai tsaye. Tun daga wancan lokacin, kallon “Shagalin murnar bikin bazara” tare da daukacin iyali a jajibirin sabuwar shekara ya zama wata muhimmiyar al’adar sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa, kamar yin dumplings da manna takaradun fatan alheri na bikin bazara. Shirye-shiryen masu ban sha’awa da aka gabatar a cikin “Shagalin murnar bikin bazara” na tsawon shekaru, sun zama abin tunawa da bikin bazara ga daruruwan miliyoyin Sinawa.

Shagalin murnar bikin bazara na shekarar 2023 yana manne da manufar dake hade da tunani da fasaha, da koyi daga kyawawan al’adun gargajiya na kasar Sin, da rayuwa ta hakika, da kuma hazakar wayewar kasashe daban-daban na duniya, tare da fasahohin zamani da fasahar haske da inuwa, don nuna shirye-shiryen kade-kade da raye-raye, da wasannin kwaikwayo masu ban dariya, da wasannin gargajiya, da wasan Kungfu da sauransu. Abin lura shi ne, sakamakon sabbin fasahohi masu yawa da aka yi amfani da su, shagalin na bana ya samu sabbin ci gaba a fannin tasirin sauti da hoto.

A ranar 21 ga wata, a jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, shagalin murnar bikin bazara na shekarar 2023 ya bi Sinawa dake duk fadin duniya don bayyana fatansu a sabuwar shekarar zomo, tare da maraba da sabuwar shekara mai kyakkyawar makoma. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
Ban Taba Jin Kunyar Sana’ar Sayar Da Maganin Mata Ba -Sahura Haruna

Ban Taba Jin Kunyar Sana’ar Sayar Da Maganin Mata Ba -Sahura Haruna

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version