ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ban Taba Jin Kunyar Sana’ar Sayar Da Maganin Mata Ba -Sahura Haruna

by Leadership Hausa
3 years ago
Maganin Mata

A wanan makon wakiliyarmu Bushira Nakura ta tattauna ne da Sahura Haruna Isma’il Meguza wata mai sana’ar sayar da maganin mata, ta yi bayanin yadda ta samu kanta a cikn sana’ar da kuma irin kalubalen da ta fuskanta a yayin da ta fara sana’ar da kuma burin da take da shi a nan gaba.

Ga dai yadda hirar ta kasance:

Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanki da kuma sunan da aka fi saninki da shi, tare da dan takaitaccen tarihinki.

ADVERTISEMENT

Sunana Sahura Haruna Isma’il Meguza, an haifeni a Fage ashekarar 1987, na yi karatun addini dana Boko daidai gwarwadon iko.

Me ya ja hankalin ki har kika fara sana’ar sayar da magungunan mata?

LABARAI MASU NASABA

Aure Ba Ya Ruƙuwa Sai Da Sana’a

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Ai ita wannan sana’a ce me cike da lada da kuma daidaito ga ma aurata  gefe guda kuma sana’a ce da zaka sami rufim asiri.

Ya farkon fara sana’arki ta kasance,ta wacce hanya kika bi har kika fara, kuma ya kika ji a lokacin da zaki fara, kasancewar wasu na son yin irin sana’ar amma kuma suna tsoro ko kunya, shin kema kin tsinci kanki a irin wannan matsalar ko kuwa?

Tabdijan a lokacin da zan fara don ba komai ma na iya ba saidai na je gun yayata na karbi magungunan da yawa  na yi wasu da kaina na hada nazo na jerasu a kan tebur sai mata masu sari da masu siyan daidai su fara dauka wasu su kawo kudi daidai wasuma bazan sake ganinsu ba.

Gaskiya ban ji kunya ba tunda mu munga wasu daga iyaye mu da yayye suna yin wannan sana’ar mun taso a cikinta gaskiya, in ana maganar kunya sai wanda ya shigo harkar kai tsaye shi ne zai rinka jin kunya kafin ya waye a ciki.

Daga lokacin da kika fara sana’ar kawo yanzu za ki kai kamar shekara nawa kina yi?

To a yanzu dai gaskiya daga lokacin dana fara sana’ar magani zan kai shekara 16 in ma ban fi ba.

Ke kike hada magungunan da kanki ko kuwa sarowa kike yi, sannan ke ma ki dora naki ribar ki sayar, ya abin yake?

Alhamdulillahi yanzu kam ni nake yi, sai dai wani abin bani dashi na kan sara daga wasu.

Ya kike ganin yadda karbuwar sana’ar take kasancewa ga su masu sayan, shin kwalliya na biyan kudin sabulu kuwa?

Alhamdulillahi, a gaskiya  sana’ar indai za a yi aiki me kyau to ba damuwa za ta karbu , gaskiya kwalliya na biyan kudin sabulu.

Ta wacce hanya kike bi wajen ganin kin bunkasa kasuwancinki?

Ta hanyoyin sadarwa (social media) Facebook, WhatsApp, TikTok, dadai sauransu.

Za ki ji likitoci da wasu masana na magana game da ire-iren wadannan magunguna wanda mata ke amfani da su, na cewar suna iya kawo wa mace matsala, me za ki ce a kan hakan?

Haka ne ai akwai wanda basu san me suke ba su dai kawai su sami kudi, yana da kyau kowace mace tasan me za ta saya tai amfani da shi ta san kuma daga wa ta saya gudun samun matsala.

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta ga su masu siyen, musamman wajen karbar bashi kuma aki biya, ko kuma a saya a samu matsala, ko makamancin haka, me za ki ce a kan hakan?

To gaskiya na fuskanci kalubale da dama a yanzu haka akwai wayanda suka sa na tura musu kaya da zummar in sun karbi kaya za su sami kudin amma har yau ba amo ba labari wata ma ta yi ‘Blocking’ dina haka na hakura kuma ba kudi kadan ba, masu kanana ma kuwa ba’a magana.

Wadanne irin nasarorin kika samu game da wannan sana’a taki?

Alhamdulillahi na samu nasarori da dama da ba za su kirgu ba sai dai muce Alhamdulillahi.

A ina kike gudanar da kasuwancinki, akwai wani waje ne da kika ware na musamman ko kuwa a cikin gida kike yi?

Ina yi a gida da kuma ‘Social media’ kamar yadda na fada miki tun da farko

Mene ne burinki na gaba game da wannan sana’a taki?

Allah ya kara sa mana albarka a sami babban shago asa kayyakimmu a samin masu kula da gurin

Kamar wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba?

Mace ta farko dana taba turawa maganin kashe meku ya wato (kaikayi da kurajen gaba) kamaru ta yi min kyautar danayi mamaki,  dama dana gaya mata kudin  magani ta ce ita ba kudin take son jiba indai na tabbatar magani mai kyau ne in biya kudin mota in aika mata haka na biya na aika Aiko naji dadin godiyar da tayi da jin dadin data yi sannan ta yi min ninkin bani kin kudin abin dana aika mata na ji dadi kuma na yi farin ciki.

Bayan sayar da magunguna da kike yi, shin kina wata sana’ar ne ko iya ita kawai kike yi?

Na dan taba rubutun littafi  kuma yanzu haka ina hadawa dasu turaran wuta dana humra.

Idan kina wata sana’ar ya tsarin kasuwancin yake kasancewa, kuma ya bambancin yake kamar wajen yadda sana’ar take  kawo kudi da sauransu?

Akwai bambanci mabayyani gaskiya domin shi magani dabanne wata daga uwa duniya zatace naki takeso gaskiya magani yafi tafiya yadda akeso

Wanne kira za ki yi ga matasa musamman mata wadanda ba sa sana’a ba su da abin yi, har ma da manya na gida, me za ki ce a kan su?

To sana’a dai rufin asiri ce musamman ma ga mata domin tallafawa iyayenki, ‘Yan uwa, mazajen da yara Dake kanki domin in kina sana’a ba sai kinyi yar mirya abakiba hasalima ke Zaki tallafi wasu, suttura da kayan kwalliya da Kawa sai Wanda kika so.

Ko akwai wani kira da za ki ga gwamnati game da masu kokarin yin sana’a?

A tallafa musu don su samu su tsaya da kafafunsu.

Me za ki ce da wannan shafi na Adon Gari?

Godiya ta musamman ga wannan shafi na adon gari

Me za ki ce da Jaridar Leadership Hausa?

Allah ya kara daukaka wannan jarida ta LEADERSHIP HAUSA kuma Allah ya karo dumbin masoya   ya biya musu bukatnsu na alheri na gode.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Gaisuwa ta musamman ga iyayena, yayata Maman Nura me kayan mata, kanwata Maman Al-ansar jigon mata,da sauran ‘yan uwa da abokan arziki da kuma Malama Bushira Nakura. Na gode

Muma mun gode

Maganin Mata
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

Aure Ba Ya Ruƙuwa Sai Da Sana’a
Labarai

Aure Ba Ya Ruƙuwa Sai Da Sana’a

January 24, 2026
Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC
Sana'a Sa'a

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera
Sana'a Sa'a

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

February 1, 2025
Next Post
Yadda Ake Kafa Kamfanin Burodi

Yadda Ake Kafa Kamfanin Burodi

LABARAI MASU NASABA

Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Lalata Da Ƙaramar Yarinya: Kotu Ta Yanke Wa Tsoho Mai Shekara 75 Hukuncin Ɗaurin Shekara 10 A Ribas

July 15, 2026
Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin

July 15, 2026
‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.