Rahotanni daga hukumar kwastam ta birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin na cewa, zuwa ranar 3 ga watan Maris din da muke ciki, yawan ridin da aka shigo da su daga Afirka ta tashar jiragen ruwan Waigaoqiao ta Shanghai, ya kai ton 1845 gaba daya, wanda ya karu har sau 4.3 akan na bara.
Kasar Sin babbar kasuwa ce ta farko, da take shigowa da ridi daga kasashen Afirka a halin yanzu, kana kuma tashar Waigaoqiao ta zama babbar tashar dake shigowa da ridin zuwa Shanghai. A watannin Janairu da Fabrairun bana, akasarin ridin da kasar Sin ta shigo da su daga Afirka, sun fito ne daga kasashen Mali, da Togo, da Mozambique, da Nijar, da kuma Tanzaniya.
Alkaluman hukumar kwastam ta birnin Shanghai sun shaida cewa, a watannin Janairu da Fabrairun bana, tashoshin jiragen ruwan birnin sun shigo da nau’o’in amfanin gona na Afirka da yawansu ya zarce ton dubu 40, ciki har da ridin, da darajarta ta zarce dalar Amurka miliyan 100. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp