• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi: Siyasar Ubangida Da Zaben Shekarar 2023

byIdris Aliyu Daudawa
3 years ago
Siyasar

Ubangida, Maigida, Jagora, Na- gaba, ana nufin wani jigo ne sunan da za a iya kiransa dalili, shi ne ya ga shekaran jiya, jiya, yaga yau, gobe ma yana sa ran cikin ikon Allah zai iya ganinta.

Ana kuma koyon abubuwa da yawa daga wurinsa, Ubangida ya kasu nau’i daban-daban, wadanda suka hada da na Siyasa, Kasuwa, wata sana’a da dai sauran makamantansu.

  • Ko Makiyan Buhari Sun San Aikin Da Ya Yi Yafi Na Gwamnatocin Baya -Minista
  • NIS Ta Cafke Dillalan Makamai A Iyakar Nijeriya Da Kamaru

Daga wurin shi ne ake koyon al’amuran daban-daban na bangarori na rayuwa, saboda an san cewa shi ya kware ne a cikin al’amarin, ko al’amuran don haka ne kuma ake zama, ko tarayya da shi domin a samu damar koyon wani abu daga wurinsa.

Dalilin koyon abin shi ne domin wanda yake bin shi sau da kafa cikin kowanne hali yana son koyon wani abu ne ko wasu abubuwa da yake ganin zuwa gaba za su amfane shi a rayuwa.

Amma kada dai in dauki masu karatu zuwa wani wuri mai nisa domin kada a kauce ma shi maudu’in wato Siyasar Ubangida A Zaben 2023, tunda yanzu sanin kowa ne an riga an shiga harkokin tunda an yi zabubbuka fidda gwani na ‘yan takara da suka hada da na majalisar Jiha, tarayya, majalisar dattawa, gwamnoni da kuma ‘yan takarar shugaban kasa.

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

Wadannan tuni aka dade da zaben su ta fitar da gwani ta hanyoyi daban- daban.

Babban abinda ya rage yanzu shi ne ranar da za a fara yakin neman zabe na mukaman siyasar daban–daban wanda shi ne lokacin da ake jira kowa kuma dole ne ya jira shi, sanin kowa ne bai shi bai jiran kowa.

An dai taka salon siyasa lokacin da aka yi zabubbukan na fidda gwani, inda aka bullo da `wata hanya duk da yake dai ba bakuwa bace an dade da sanin ta.

Wannan ba wani abu bane illa wakilai ko kuma ‘Delegates’ kamar yadda wasu suka sani.

Wani salo ne inda wasu daga cikin ‘delegate’ suka kasance ba ‘yan siyasa ba ne wadanda da suke da fada aji, an dai bulla da hanyar ne domin a cakusa ma wasu zuciya.

Hausawa ko masu iya magana sun ce “Komai girman Kurciya idan bata da Fiffike ‘ya ce” wannan shi yasa ‘yan siyasa wadanda su ba kowan–kowan ba ne suke rabuwa da inuwar wasu, domin su samu zuwa tudun mun tsira.

Ubangida a siyasa shi yake amfani da abubuwa da dama domin cimma burinsa ko wanda yake son ya cimma burin nasa. Idan muka duba tasirin Ubanningida.

Iyayen gida a siyasa sai mu kalli yadda aka gudanar da zabubbukan fida gwani na manyan jam’iyyun siyasa biyu na Nijeriya APC da PDP.

Wadanda ya yi takarar dasu wasu yaransa ne a siyasance.

An gani da jin yadda ta kaya lokacin da aka yi zabubbukan idan aka fara da PDP, idan da ba ayi amfani da tasirin Ubangida a siyasa ba ai da Atiku Abubakar bai samu damar lashe zaben fidda gwanin ba, sai da aka yi wa Aminu Waziri Tambuwal magana daga sama cewa ya janye daga takarar, wakilansa suka kadawa Atiku daganan ya samu nasarar lashe zaben.

Hakanan shi ma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da wasu daga cikin yaransa ne ya yi takarar zaben fidda gwanin kamarsu Sanata Ahmad Lawan Shugaban majalisar dattawa, da mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo, sai da suka fafata daga baya suka gane ashe ruwa ba tsaran Kwando ba ne.

A Arewacin Nijeriya idan kuma aka kalli wasu Jihohi ana iya ganin tasirin da Ubangida ya fara yi a siyasa tun ma kafin a zo zaben shekara ta 2023.

Akuya ko bata haihuwa tafi Kare mai girman gwamnan Jihar Kaduna Nasiru Ahmed El Rufa’i shi ma yanzu babban Ubangida ne a siyasar Jihar Kaduna kowa ya ga irin rawar daya taka shekarun da suka gabata a siyasance, kai karshen magana ma dai yanzu Sanata Uba Sani wanda na hannun damarsa ne, shi ne dantakarar gwamna na jam’iyyar APC, wanda shi ma dan siyasa ne sai dai El Rufa’i ya kara wayar ma shi da kai kan al’amarin siyasa.

Jihar Jigawa akwai Sule Lamido tsohon gwamnan Jihar wanda biyu daga cikin ‘ya’yansa suna takara, daya na takarar gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar PDP, sai ‘yarsa da take takararar majalisar wakilai ta tarayya,shi ma kansa yana takarar Sanata.

Sai kuma Jihar Zamfara inda akwai tsofaffin gwamnonin Jihar da suka hada da Abdul’aziz Yari, Sanata Sani Ahmad Yariman Bakura, Aliyu Shinkafi, Sanata Aliyu Marafa da gwamna mai jan ragamar Jihar yanzu Bello Matawallen Maradun, duk dai Ubannin gida ne na siyasa a Jihar.

Ita ma Jihar za ta kasance allura cikin ruwa mai rabo ka dauka’yan siyasa za su rika zawarcinta.

Jihar Kano ita ma Jiha ce wadda tana da Iyayen gida ko Ubannin gida a siyasa idan aka tuna da irin fafutukar da marigayi Malam Aminu Kano Shugaba kuma dantakarar jam’iyyar PRP a zaben shekarar 1979,ko shakka babu Maigida ne na Limamin canji marigayi Alhaji Abubakar Rimi.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Sanata Ibrahim Shekarau duk tsofaffin gwamnoni ne, akwai Sanata mai ci yanzu, uwa uba kuma ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kowa ya san rawar daya taka yake kuma kara takawa a siyasar Jihar Kano, shi yasa kamar Jihar Zamfara, ita ma ba a san maci tuwo ba sai idan miya ta kare tukuna.

Ganduje ma yana da dan takarar gwamna na APC a zaben 2023 Dakta Gawuna da mataimakinsa Sulen Garo, akwai dai abubuwa da yawa da za su iya faruwa a zaben 2023 a Jihar ta Kano abar hange ce musamman ma yadda aka samu sauyin jam’iyya na Sanata Ibrahim Shekarau.

Haka dai tasirin Ubangida a siyasa al’amarin ya fara daukar hankalin wasu mabiya harkokin siyasa da ma su ‘yan siyasar tun ma kafin lokacin ya zo.

Wannan shi yasa Jihar Kwara idan ana maganar Ubangida ne a siyasa ya sa ba za a taba mantawa da marigayi Sanata Abubakar Sola Saraki ba saboda irin gudunmawar daya bada, a karkashin shiwasu sun koyi siyasa sun zama Malamanta.

Jihohin Sakkwato da Bauchi ba za a manta dasu ba su mamusamman idan aka tuna da marigayi Firayim Minista Nijeriya na farko marigayi.

Abubakar Tafawa Balewa,da Firimiyan Arewa Alhaji Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato.Hakika a siyasar Nijeriya ba za a taba mantawa dasu ba.

Daga sashen Kudu ma akwai irin su akwai irinsu Christ Uba da Andy Uba a sashen Kudu maso gabashin Nijeriya suma ba kanwar lasa ba ne, can ne kuma Dakta Nmandi Azikwe shugaban jamhuriya ta farko ga Dakta K.O. Mbadwe da dai sauransu.

Koma dai menene siyasar Uban gida a Nijeriya tana da alkhairinta da rashinsa, wasu na taimakawa wajen yin ayyuka masu dacewa su Ubannin gidan yayin da wasu sai dai a rika sace kudin kasar ko Jihar tare da su. Su hana ruwa gudu har sai zuwa lokacin da aka biya masu bukata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
Labarai

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

October 2, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

September 28, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas
Siyasa

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Next Post
Abubuwa 5 Da Ke Sa Ido Fari Mai Ban Sha’awa

Abubuwa 5 Da Ke Sa Ido Fari Mai Ban Sha’awa

LABARAI MASU NASABA

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version