• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi: Ya Kamata A Dauki Batun Makamashi Na Kasashen Afirka Da Muhimmanci Don Tinkarar Matsalar Sauyin Yanayin Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
Afirka

A yau ne aka rufe taron masu ruwa da tsaki kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 27 (COP27), taron da aka yi shirin kammala shi a ranar 18 ga wata, wanda kuma aka jinkirta shi sakamakon sabanin ra’ayin da bangarori daban daban suka samu ta fannonin tattara kudin biyan tarin asarar da kasashe masu tasowa suka tabka sakamakon sauyin yanayi da ma burin da ake neman cimmawa wajen rage fitar da iskar Carbon.

Sai dai abin farin ciki shi ne, a karshe kasashe daban daban sun cimma daidaito, game da kafa asusun biya hasarorin da aka tabka sakamakon sauyin yanayi, don taimaka wa kasashe masu karamin karfi wajen tinkarar matsalar sauyin yanayin duniya.

  • Masana: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Karfin Afirka A Fannin Aikin Injiniya

Da wuya a cimma daidaito tsakanin kasashe masu ci gaba, musamman Amurka da sauran kasashen yamma, da ma kasashe masu tasowa musamman kasashen Afirka, ta wadannan fannoni biyu, wato tattara kudaden biyan hasarorin da kasashe masu tasowa suka yi sakamakon sauyin yanayi da ma burin da ake neman cimmawa wajen rage fitar da iskar Carbon, sai dai duniyarmu daya ce, kuma “yadda kasashe masu sukuni za su taimaka wa kasashe masu tasowa wajen samun ci gabansu” da ma “yadda kasashe masu ci gaba da kasashe masu tasowa za su dauki mabanbantan nauyi wajen tinkarar sauyin yanayi”, abu ne da ake neman cimmawa wajen daidaita matsalar sauyin yanayi.

Yawan hayaki mai dumama yanayi da kasashen Afirka suka fitar ya kai kaso 4% ne kawai na hayakin da ake fitarwa a duniya baki daya. Matsalar sauyin yanayi ta haddasa musu munanan hasarori, ba laifinsu ba ne, don haka, bai kamata kasashe masu ci gaba su koma gefe suna kallo ba kawai.

A sa’i daya kuma, a baya kasashen Afirka ba su bunkasa sosai ba, kuma hayakin da suke fitarwa bai taka kara ya karya ba. Don haka, a gaba ma bai kamata su dauki nauyi iri daya da na kasashe masu arziki ba.

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kasancewarta ta biyu a duniya ta fannonin fadin filaye da ma yawan al’umma a duniya, nahiyar Afirka na taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar sauyin yanayin duniya, don haka ma, ya zama dole a fara taimakawa kasashen Afirka wajen daidaita batun makamashi.

Yawan wutar lantarki da ake amfani da shi a gaba dayan kasar Senegal bai kai yawan wutar lantarki da ake amfani shi a na’urorin wasa na zamani a jihar California ta kasar Amurka ba, kuma kaso 3% na al’ummar kasar Nijeriya suke amfani da na’urar sanyaya daki (Air Conditioner).

A kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, akwai mutane kusan miliyan 600 da suke rayuwa ba tare da samun damar yin amfani da wutar lantarki ba. Ina dalilin haka? Lallai matsalar karancin makamashi da kasashen Afirka ke fuskanta matsala ce ta rashin samun ci gaba. Don haka, muddin dai kasashen Afirka suka tabbatar da ci gabansu da ma damar amfani da makamashi, za su iya samun kwarewar fuskantar sauyin yanayi.

Idan har ana son magance matsalar sauyin yanayi, to, ya zama dole a rage yin amfani da makamashin dake fitar da iskar Carbon. Don haka, a gun taron COP27, kasashe masu arziki sun fi mai da hankali a kan shirin samar da iskar gas na kasashen Afirka, a maimakon matsalar sauyin yanayi da ke addabar kasashen Afirka, har ma sun bukaci kasashen Afirka da su dakatar da yin amfani da albarkatun da suke da su.

Amma abin dariya shi ne a sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine, kasashen yamma ko kadan ba su ambaci abin da ya shafi rage iskar Carbon da suke fitarwa ba, har ma suka koma yin amfani da kwal da katako da suke iya kara fitar da iskar Carbon. Kasashen Afirka suna da hakkin raya kansu da ma kyautata rayuwar al’ummarsu, bai kamata wasu kasashe su nuna musu yatsa a kan wannan batu ba, kuma bai kamata su nuna ma’auni biyu ba.

Duk da cewa an cimma daidaito game da kafa asusun biyan hasarorin da aka samu sakamakon sauyin yanayi a gun taron COP27, amma ba a tabbatar da wadanne kasashe ne za su zuba kudaden ba, don haka akwai sauran rina a kaba a fannonin yawan kudaden da za a tara da ma yadda za a raba kudaden.

Duk da haka, muna da imanin cewa, a yayin da ake fuskantar sauyin yanayi, ya kamata kasa da kasa su hada kansu, kuma bai kamata a manta da kasashen Afirka ba, balle ma a bar su a baya ba. (Lubabatu Lei)

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
Daga Birnin Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Next Post
Mataimakin Shugaban Jami’ar Kwara, Akanbi, Ya Rasu Yana Da Shekaru 51

Mataimakin Shugaban Jami'ar Kwara, Akanbi, Ya Rasu Yana Da Shekaru 51

LABARAI MASU NASABA

gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

October 18, 2025
Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.