• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi: Yadda Sin Ke Nisantar Da Duniya Daga Haɗari

by CMG Hausa
2 years ago
Sin

Wasu ƙasashen yammacin duniya suna da ɗabi’ar ɗaiɗaikun ra’ayoyin da suka ƙirƙiro don biyan buƙatunsu na cikin gida. Misali na baya-bayan nan ya kasance kalmar “de- risking” wato “A guji haɗarin mu’amala da Sin”, wanda a hakikanin gaskiya “rarrabuwa” suke nufi, wannan ita ce da’awarsu asirce, dunkulewar duniya waje guda tamkar barazana ce a gare su. Duk wani mai hankali zai gane cewa wannan da’awar tasu, tsohon ruwan inabi ne kawai a cikin sabon kwalba.

Shekaru uku da suka gabata, ƙungiyar Eurasia, ɗaya daga cikin manyan masu ba da shawara kan haɗarin siyasa a duniya, ta kira “Tsarin Rarrabuwa ta Amurka” babbar haɗari dake fuskantar duniya. A maimakon mayar da hankali kan rikici cikin gidanta, Amurka ta zaɓi sanya wa wasu laƙabi da “haɗari” tare da zarge su da matsalolinta. Haɗarin Amurka a zahiri shi ke haifar da haɗari ga duniya, a yayin da ƙasar Sin ke nisantar da duniya daga irin wannan haɗarin.

  • Mizanin GDP Na Sin Ya Karu 5.5% a Farkon Rabin Shekara Na Bana

Ƙasar Amurka na da dogon tarihi na aƙidar “wariya” tun daga lokacin da ta samu ‘yancin kai. Gaskiyar ita ce: Amurka na kaucewa alhakin ƙasa da ƙasa da ke kanta, shi ya sa take shiga cikin cibiyoyi da yawa a daidai lokacin da yin hakan ya dace da son ranta. Yayin da take iƙirarin cewa ba ta da tsangwama kuma ba ta da hannu a cikin al’amuran wasu ƙasashe. Amurka na ci gaba da gina ƙananan ƙungiyoyi irin su AUKUS, QUAD, Five Eyes da G7 ɗauke da takamamman maƙasudi a cikin zuciya, da ya kunshi rarrabuwa, da adawa da rashin zaman lafiya.

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Saɓanin haka, ƙasar Sin ta ƙuduri aniyar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama, kuma ta tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya da aiwatar da tsarin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa tsawon shekaru da dama. Ta zama abokiyar tattaunawa ta ASEAN, da shiga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama, da ƙaddamar da bankin zuba jari na kayayyakin more rayuwa na Asiya, da ba da shawarwari ga jama’ar duniya. Da gabatar da shirye-shirye irin su shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya (BRI), da Shirin Ci Gaban Duniya, da Shirin Tsaro na Duniya da Tsarin Wayewar Duniya, da dai sauransu. Yayin da wasu ƙasashe suka janye daga wajibcin ƙasa da ƙasa da yarjejeniyoyin da ƙungiyoyi, ƙasar Sin ta na ɗaɗa kira da a kara hadin kai, kuma ba ta taɓa yin watsi da nauyi da ke kanta a matsayin babbar ƙasa ba.

“Dala ita ce kudinmu, amma matsala ce gare ku.” Wannan sanannen ƙa’ida ce a Amurka. Tsawon shekaru, a ƙarƙashin mulkin dala, Amurka ta haddasa hauhawar farashin kayayyaki ga sauran ƙasashen duniya, ta haifar da rikicin kuɗi da na bashi a wasu ƙasashe da kuma kara haɗarin tattalin arziki da kuɗi na ƙasa da ƙasa. Ta ci gaba da yin amfani da rinjayen dala don yin “ta’addanci na kuɗi.” Ta kakkaba wa ƙasashe kusan 40 takunkumin tattalin arziki, lamarin da ya yi illa ga kusan rabin al’ummar duniya. Bugu da ƙari, Amurka tana yin amfani da fa’idodinta na fasaha ta hanyar gina “ƙananan dandali masu manyan shinge” kamar “Chip 4 alliance” da “Clean Network initiative” – wanda har abokan hulaɗarta ba za su amfana da waɗannan shirye-shiryen ba.

Ƙasar Sin, ba kamar Amurka ba, tana da ikon samun wadata kuma tana baiwa sauran ƙasashen duniya damar ci gaba a cikin wadatar da ta samu. Tare da halartar ƙasashe 150 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa 30, BRI ta samar da ayyukan haɗin gwiwa sama da 3,000, da samar da ayyukan yi na kusan 420,000, tare da fitar da kusan mutane miliyan 40 daga kangin talauci. Layin dogo na Mombasa-Nairobi, da layin dogo na kasar Sin zuwa Laos da babban layin dogo na Jakarta-Bandung sun kawo ci gaba na gaske ga al’ummomin yankin. Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su na ƙasa da ƙasa na ƙasar Sin wato CIIE, ya kasance wani dandali mai inganci ga kamfanoni a duk duniya, don cin gajiyar ci gaban tattalin arzikin ƙasar Sin.

Kamar yadda Jeffrey Sachs, farfesa kuma darektan cibiyar raya ci gaba mai dorewa ta jami’ar Columbia, ya ce a dandalin dimokuradiyya na Athens 2022, kasar Sin ta samu nasarori masu ban mamaki a cikin shekaru 40 da suka gabata, don haka ya kamata mu “yi farin ciki da nasarorin da ƙasar Sin ta samu, ba wai mu tsorata ba.” (Yahaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
Daga Birnin Sin

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Daga Birnin Sin

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
Daga Birnin Sin

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Next Post
Farashin Abinci Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Zuwa Kashi 22.79 A Cikin Dari

Farashin Abinci Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Zuwa Kashi 22.79 A Cikin Dari

LABARAI MASU NASABA

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
Sin

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.