Kwanan nan, a birnin Beijing da nake zaune, mutane da motoci na kara kai komo a kan tituna kwatankwacin kimanin makwanni biyu zuwa uku da suka wuce.
A wani titin mai yawan gidajen cin abinci a dab da unguwar da nake zama kuma, mutanen da ke zuwa don cin abinci suna ta karuwa, hakan ma kantuna da gidajen sinima da ma sauran wuraren shakatawa.
Abin da ke faruwa a birnin Beijing haka ma lamarin yake a sauran sassan kasar Sin, ga dukkan alamu, sakamakon matakan da gwamnati ta dauka na kara kyautata ayyukan kandagarkin cutar Covid-19, al’umma na komawa ga rayuwar da suka saba a baya.
Bisa tushen nasarorin da aka samu wajen kandagarkin cutar Covid-19 cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta bullo da jerin matakai na kara kyautata ayyukan kandagarkin cutar Covid-19 tun watan da ya gabata.
A kwanakin baya kuma, ta sanar da sauya matakin yaki da cutar daga rukunin A zuwa rukunin B, wanda za a fara aiwatar da shi tun ranar 8 ga wata mai zuwa.
To, duk wadannan matakai ne da gwamnatin kasar Sin ta dauka bisa la’akari da yanayin cutar da sauran fannoni a kimiyyance, a wani kokari na daidaita aikin kandagarkin cutar da ma bunkasuwar tattalin arziki da zaman al’umma, kuma tana daukar matakan ne bisa manufarta ta ainihi, wato dora jama’a a gaban kome.
A hakika, cikin shekaru uku da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta nace ga wannan babbar manufarta ta dora jama’a a gaban kome, inda ta ceton miliyoyin rayukan al’ummar kasar duk da asarorin tattalin arziki da ta fuskanta, ta kuma kiyaye kason mutuwar mutane sakamakon cutar a wani matsayi mafi kankanta a duniya. Mashahurin masanin harkokin kasar Sin na Birtaniya John Ross a tattaunawar da ya yi tare da wakiliyarmu a kwanan baya, ya yi nuni da cewa, kasar Sin ya cimma gaggaruman nasarori wajen kiyaye lafiyar al’ummarta da kuma ceton rayukansu. Ya ce, “Sama da mutane miliyan daya cutar ta halaka a kasar Amurka, idan aka kwatanta wannan kaso na mutuwa a kasar Sin, lallai yawan mamata sakamakon cutar a kasar ka iya kaiwa sama da miliyan 4.6. Don haka, muna iya cewa gwamnatin kasar Sin ta ceto rayukan mutane sama da miliyan 4.”
Ta hanyar daukar tsauraran matakai masu inganci wajen kandagarkin cutar, kasar Sin ta samu isasshen lokaci na nazarin magunguna da samar da rigakafi cikin shekaru uku da suka wuce, a yayin da cutar Covid-19 ma ta yi ta sauyawa zuwa nau’in Omicron wadda ta kara karfin yaduwa amma irin barnar da take haifarwa ga lafiyar mutum ba ta kai ta ainihin cutar ba, inda yawan wadanda suka harbu da cutar da ke nuna alamu masu tsanani da wadanda cutar ta halaka duk sun ragu kwarai da gaske.
Wannan ya sa, gwamnatin kasar Sin ta daidaita matakanta na kandagarkin cutar. A sa’i daya kuma, kasar ta yi wa akasarin al’ummarta cikakken rigakafi, ta kuma tara dimbin fasahohi na yaki da cutar, tare da inganta aikin nazarin magunguna da kiwon lafiya, matakan da suka aza harsashi mai inganci ga kyautata ayyukan kandagarkin cutar.
Ba shakka, duk kasar da ta sassauta matakan kandagarkin cutar, za ta samu saurin karuwar masu cutar da ma wasu matsaloli ta fannin kiwon lafiya na dan gajeren lokaci, abin da kasar Sin ma take fuskanta ke nan a sakamakon daidaita matakanta, sai dai hakan ya zama dalilin da wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma ke zargin kasar da su, abin dariya shi ne, a baya, wadannan kafofi ne suke zargin kasar Sin da daukar matakan kandagarki fiye da kima. Don haka, matsalar ba wai ita ce me kasar Sin ta yi, sabo da sukar kasar shi ne abin da ya dace ga kasashen ta fannin siyasa.
Ni kaina tare da wasu iyalaina da abokaina a kwanakin baya ma mun harbu da cutar, sai dai akasarinmu ba mu nuna wata alamar cutar ba ko kuma alamu masu sauki ne muka nuna, kuma bayan kimanin sama da mako daya da muka killace kanmu a gida mu ka huta, sai mu ka warke kuma mu ka koma bakin aiki da ma rayuwar da muka saba.
’Yan kwanaki kadan suka rag a shiga wata sabuwar shekara, gwamnatin kasar Sin yanzu na kokarin daukar matakai don daidaita matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu, kuma al’ummar kasar ma na sa ran rungumar sabuwar rayuwarsu a cikin sabuwar shekara. (Lubabatu)