ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi:Tarkon Bashi Ne Ko Kuma Na Yaudara?

by CMG Hausa
3 years ago
Bashi

A sakamakon komadar tattalin arzikin duniya, da kuma faduwar farashin mai da na sauran kayayyaki a fadin duniya cikin ‘yan shekarun baya, kudin shigar kasashen Afirka ya ragu, lamarin da ya haifar da matsalar bashi gare su, baya ga kuma annobar Covid-19 da ta yi ta addabar duniya, wadda ta kara tsananta matsalar.

Ganin haka ya sa kasashen yammacin duniya suke ta yayata zancen wai “tarkon bashin kasar Sin” , tamkar kasar Sin ce tafi kowa bin kasashen Afirka basussuka, wadda kuma take daukar alhakin matsalar da suke fuskanta.

  • Wayar Da Kai: INEC Za Ta Hada Hannu Da Kungiyar ‘Darika Awareness Forum Katsina’ 

Sai dai alkaluma ba su karya. Wani rahoton da cibiyar nazari ta “Debt Justice” ta kasar Birtaniya, ta fitar a kwanan baya ya yi nuni da cewa, bisa ga kididdigar da bankin duniya ya yi, daga cikin basussukan da gwamnatocin kasashen Afirka suka ci, kaso 12% na kasar Sin ne, a yayin da kasashen yamma, musamman ma sassa masu zaman kansu suke binsu kaso 35%.

ADVERTISEMENT

A sa’i daya kuma, kasar Sin ta samar da basussuka ne kan kudin ruwan da ya kai kaso 2.7%, a yayin da kudin ruwan da kasashen yamma suke karba ya kai kaso 5%. Lallai kamar yadda Tim Jones, babban jami’in cibiyar ta “Debt Justice” ya fada, “shugabannin kasashen yamma suna dora laifin matsalar bashi kan kasar Sin ne, don kawar da idon al’umma.

A hakika, bankuna da kamfanonin kula da jari da na cinikin mai nasu sun fi daukar alhakin.”
Ban da haka kuma, Sin da kasashen Afirka sun sha bamban sosai, duk da cewa dukkansu na bin kasashen Afirka basussuka.

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

Na farko, burin da suke neman cimmawa ba daya ba ne. Kasar Sin ta fi mai da hankali a kan bunkasuwar kasashen Afirka cikin dogon lokaci a yayin da take samar musu basussuka, don haka, ta fi samar da basussukan fannonin kere-kere, da ma manyan ababen more rayuwa, har ma ribar da hakan ya samar tuni ta zarce basussukan, a yayin da kasashen yamma suka kasa sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin Afirka, har ma sun sa su kara shiga kangin talauci, kuma hakan suke ta kara neman basussuka daga wajensu.

Na biyu kuma, kasar Sin na aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ne bisa zaman daidaito, ba tare da tsoma baki cikin harkokin gidansu, don haka ma, ba ta taba gindaya sharudan siyasa ba a yayin da take bin su basussuka, kwatankwacin yadda kasashen yamma su kan gindaya sharudan siyasa, da suka shafi hakkin bil Adam, da gyare-gyaren dokoki da makamantansu, a yunkurin tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen bisa ga basussukan da suka samar.

Na uku, kullum kasar Sin na dora muhimmanci a kan saukaka wa kasashen Afirka matsalar basussuka. A tarukan dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka(FOCAC) , ta sha soke basussuka maras ruwa da take bin gwamnatocin kasashen Afirka, da suke matukar fama da matsalar bashi wadanda suka kasa biya, baya ga kuma yadda take kokarin shiga hadin gwiwar sassa daban daban kan batun bashi, har ma ta zamanto ta farko wajen yawan basussukan da ta tsawaita wa’adin biyansu daga cikin kasashen G20, kwatankwacin yadda kasashen yamma suka yi shiru game da batun tsawaita wa’adin basussukan nasu sassa masu zaman kansu ke bin kasashe mafiya fama da talauci, baya ga kuma yadda suke yayata zancen wai “tarkon bashin kasar Sin” a kungiyar G7.

Da haka muke iya gano cewa, maganar wai “tarkon bashin kasar Sin”, tarko ne kasashen yamma suka kafa don hana kasashen Afirka samun ci gaba, haka kuma yaudara ce ta lalata hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. (Mai zane:Mustapha Bulama)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 
Daga Birnin Sin

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

November 13, 2025
Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia
Daga Birnin Sin

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

November 13, 2025
Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana
Daga Birnin Sin

Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

November 13, 2025
Next Post
Wata Mata Ta Kashe Mijinta Da Wuka Har Lahira A Adamawa

Wata Mata Ta Kashe Mijinta Da Wuka Har Lahira A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

Abin Da Ya Sa NPA Ta Yi Hadaka Da ‘Snake Island Port’ -Dakta Dantsoho

November 14, 2025
Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

Shugaban NPA Ya Bukaci A Yi Hadaka Domin Cin Gajiyar Albarkatun Fannin Sufurin Afirka

November 14, 2025
Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci

November 14, 2025
Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Jan Aikin Da Ke Gaban Manyan Hafsoshin Tsaron Nijeriya

November 14, 2025
Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

November 13, 2025
Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

November 13, 2025
Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

Shugabar IOC: Gasar Wasanni Ta Kasar Sin Tana Da Babbar Ma’ana

November 13, 2025
Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

Ayyukan Kirkire-kirkire Na Kamfanonin Sin Na Kara Zama Babbar Kadara Ga Duniya

November 13, 2025
Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4

November 13, 2025
An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu

An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu

November 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.