Kwanan baya, kasar Amurka ta sanar da daukar matakan kayyade shigar baki kasar daga kasar Sin, bisa dalilin da ta bayar na wai “yaduwar cutar a kasar Sin ka iya haifar da sauye-sauyen fasalin cutar”. Amma, ko da gaske ne Amurka ta dauki matakin ne don magance cutar?
A hakika, nau’o’in cutar Covid-19 da yanzu haka ke yaduwa a kasar ta Sin, tuni sun yadu a Amurka da ma sauran wasu kasashen duniya kafin a gano su a kasar Sin. Misali, cutar nau’in BA.5 da ke yaduwa a kasar Sin ta kasance wadda aka fi fuskanta a kasar Amurka a watannin da suka gabata, baya ga cutar nau’in XBB.1.5 da kwanan baya aka gano ta a biranen Shanghai da Hangzhou na gabashin kasar, daidai ta kasance cutar da a halin yanzu taka fi yaduwa a kasar Amurka. A sa’i daya kuma, a yayin da cutar ke yaduwa a fadin duniya, sauye-sauyen fasalin cutar ka iya faruwa ko ina a duniya. Don haka, masana ilmin cututtuka masu yaduwa na kasashe da dama, sun bayyana ra’ayoyinsu na rashin yarda da daukar matakan kayyade shigar baki daga kasar Sin, baya ga kuma wasu hukumomin lafiya da suka hada da cibiyar kandagarkin cututtuka ta Turai suka bayyana cewa, bai dace ba a kayyade shigar baki daga kasar Sin.
Da haka muke ganin cewa, kasar Amurka na daukar matakin ne don siyasantar da cutar.
In mun waiwayi shekaru uku da suka wuce, za mu ga cewa, gwamnatin kasar Amurka ba ta taba mai da hankalinta a kan daidaita matsalolin da kasar ke fuskanta ta fannin kadagarkin cutar ba, a maimakon haka ma, tana ta kokarin siyasantar da cutar ne, lamarin da ya sa wannan kasar da ke sahun gaba a duniya ta fannin harkokin kiwon lafiya, ta gamu da munanan hasarorin da bai kamata ba, inda ‘yan kasar sama da miliyan 100 suka harbu da cutar, a yayin da sama da mutanen kasar miliyan 1.08 cutar ta halaka, baya ga kuma yara dubu 250 da suka zama marayu a sakamakon cutar.
Sabanin matakin da Amurka din ta dauka, hukumomin yawon shakatawa, da ofisoshin jakadanci na kasashe da dama da ke kasar Sin a kwanan baya, sun yi maraba da bakin kasar Sin zuwa kasashen su, don fatan ganin babbar kasuwar kasar ta taimaka ga farfado da tattalin arzikinsu, suna kuma fatan hada karfi da karfe tsakanin kasa da kasa, zai fitar da duniya daga mawuyacin halin da ake ciki. (Mai Zane:Mustapha Bulama)