• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shari’ar Zaɓe: Gwamnan Sokoto Ya Kori Sakatarorin Ilimi Na Jihar

by Sulaiman
2 years ago
Gwamnan Sokoto

Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto ya tsige sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 da ke jiharsa, inda ya umurce su da su mika al’amuran ofisoshinsu ga babban jami’i a kananan hukumominsu.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fitar a daren Laraba, ta ce, an tsige sakatarorin ilimin nan take.

  • Yadda Matar Shugaban DSS Ta Yi Barazanar Hana Ni Zama Gwamnan Kano –Abba Gida-Gida

Hakan ya biyo bayan zaman da aka yi a ranar Laraba a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto, wadda ta bukaci shugaban makarantar Town Model Primary School da ke Sabon Birni da ke karkashin karamar hukumar Sabon Birni, Ibrahim Abdullahi, ya ba da shaida kan karar da dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar ya gabatar a gaban kotun yana kalubalantar cancantar mataimakin  gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na tsayawa takarar gwamna a zaben 2023.

Umar a cikin karar da ya gabatar, ya na kalubalantar cancantar abokin takarar gwamna a jam’iyyar APC, Mohammed Idris Gobir, kan cewa bai halarci makarantar firamare ba.

Sbugaban makarantar ya samu rakiyar Lauyan Sa’idu Umar, S.I. Ameh SAN, zuwa zaman sauraron karar don bayarda shaida tare da gabatar da takardar shaidar shiga makarantar a 1981 da na kammala karatu a shekarar 1987, don tabbatar da cewa Gobir bai halarci makarantar ba kamar yadda ya yi ikirari.

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

Shugaban zaman sauraron kararrakin zaben, Mai shari’a Haruna Mshelia, ya amince da kwafin takardun da aka gabatar masa yayin da babban lauyan wadanda ake kara, Cif Jecob Ochidi, ya ki amincewa da takardun.

Korar da Ahmad Aliyu ya yi wa sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jim kadan bayan kammala zaman kotun, ana kallon hukuncin a matsayin ramuwar gayya da riga-kafi ga irin wannan sheda a kotun zabe, domin shi ma Gwamnan yana fuskantar irin wannan kara ta rashin halartar makaranta a kotun.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati
Labarai

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba
Labarai

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta
Manyan Labarai

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Next Post
Li Qiang: Alakar Kasashen Sin Da Faransa Tana Da Ma’ana A Duniya.

Li Qiang: Alakar Kasashen Sin Da Faransa Tana Da Ma'ana A Duniya.

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.