Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) ta ginda sharudda 17 da take neman Shugaban kasa, Bola Tinubu ya cika kafin ta amince ta janye zanga-zangan da ta fara gudanarwa a kasa baki daya.
Kugiyar NLC ta janye zanga-zangar kwanaki biyu da ta shirya bayan kwana daya da farawa. Ta ce ta amince da janye zanga-zangar ne domin tattaunawa da gwamnati ta yi.
- Kasar Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Taimakawa Jarin Waje
- Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutane 5, 10 Sun Jikkata A Hanyar Legas Zuwa Ibadan
Shugaban kungiyar kwadagon, Joe Ajaero da mukaddashin babbann sakataren kungiyar, Ismail Bello sun bayyana cewa, “Mun samu nasarar tattaunawa da gwamnati bayan gudanar da zanga-zanga a ranar farko, inda gwamnati ta yi alkawarin cewa za ta yi kokarin kare mutane da kuma ma’aikatan Nijeriya daga wannan tsadar rayuwa da ake ciki.”
A ranar farko na zanga-zangar, kungiyar kwadago ta kai ka wa shugaban kasa wasika mai taken, “Kawo karshen matsaloli da ke faru a kasar nan tun da wuri.”
Wasikar da ke dauke da sa hannun shugaban kwadago, Joe Ajaero ta yi kira ga majalisar zartarwa ta kasa da ta duba bukatun kungiyar kwadago a daidai lokacin da ‘yan kasa da ma’aikata ke fama da yunwa da kuma fatara.
Sharuddan da kungiyar kwadagon ta gindaya sun hada da samar da wani shiri na gaggawa da zai magance matsalolin da kasar nan take fuskanta a halin yanzu, wanda ta bukaci daukan matakai da za su dakile tsadar rayuwa a kasar na da kuma samun wadataccen abinci.
“Muna bayar da shawarar a sake bude dukkan iyakokin kasar nann domin samun damar shigo da abinci, siminti da kuma sauran kayayyakin bukatu. A dauki matakan kan gaggawa da za su tabbatar da samar da abinci a kasa, ciki har da tabbatar da tsare gonaki ta yadda manoma za su ci gaba da gudanar da harkokin noma.
“Muna so a dage biyan haraji ga kananan ‘yan kasuwa da ke fadin kasar nan. Cika alkawarin da aka yi mana tun a ranar 2 ga Oktoban 2023, yarjejeniyar da muka cimma tsakaninmu da gwamnati.
“Sayan matocin bas masu amfani da lantarki a dukkan jihohin kasar nan, domin sukaka harkokin sufuri da rage dogaro da man fetur.
“Dakatar da karin kudin makaranta a daukacin fadin kasar nan. Rage haraji ga masu shigo da kayayyaki da magugguna da zai rage wahalhalun da marasa lafiya ke ciki.
“Bai wa dukkan gwamnatoci umurnin biyan mafi karancin albashi da alawus-alawus na mataikata da kuma biyan kudin fansho. Biyan kudaden rage radadi ga mabukatan da aka yi wa rajista nan take. Rage harajin ma’aikata da ke daukan naira 100,000 a duk wata da kuma wadanda suke daukan kasa da naira 500,000 a duk wata.
“Cire haraji kan kayayyakin da ake amfani da su kai tsaye. Bayar da umurnin saya da amfani da kayayyakin da ake sarrafawa a Nijeriya da zai iya bunkasa kayayyakin da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa. Rage kashe kudaden gwamnati a dukkan mataki na kasar nan. Watsi da dukkan manufofin asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) da kuma bankin duniya a Nijeriya, domin ba sa yin aiki a Nijeriya sai dai suna kara mana matsin rayuwa. Gaggawan aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma kan biyan mafi karancin albashi.”