Masharhanta da yawa na yin tsokaci game da irin nasarorin da ake samu ta fuskar bunkasar ababen more rayuwa a sassan nahiyar Afirka, inda da yawa ke ganin shawarar nan ta “Ziri Daya Da Hanya Daya” ko BRI da Sin ta gabatar, na kan gaba wajen bunkasa ababen more rayuwa a kasashen Afirka, kuma shawarar ta kasance muhimmin jigo na bunkasa alakar zumunta dake tsakanin kasashen nahiyar da kasar Sin.
Wannan ma shi ne ra’ayin babban daraktan cibiyar nazarin manufofi da ba da shawarwari ta Afirka da Sin mista Paul Frimpong, wanda a baya bayan nan ya bayyana irin alfanun dake tattare da wannan shawara ta BRI, ta fuskar bunkasa ci gaban Afirka.
- Xi Ya Sha Alwashin Hadin Gwiwa Da Shugaban Jamhuriyar Congo
- Karo Na Farko Ne CIDCA Da Hukumar MDD Da Habasha Sun Sa Hannu Kan Takardar Hadin Gwiwa Da Ta Shafi Bangarori Uku
A cewar Frimpong, shawarar BRI na magance matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta a fannin samar da makamashi, da ruwa, da tsaftar muhalli, da fannonin sadarwa, da sufuri, da sauransu.
Ko shakka babu idan mun yi nazari ga kamalansu, da ma nasarorin da aka cimma na zahiri a fannin gina manyan ababen more rayuwa a Afirka, da bunkasar da nahiyar ke samu ta fuskar raya tattalin arziki, za mu ga cewa rungumar shawarar BRI da kasashen Afirka suka yi ya taimaka matuka wajen kaiwa ga nasarorin.
Tuni shawarar BRI ta taimakawa kasashen Afirka da dabarun bunkasa samar da ababen more rayuwa, ta yadda suke iya gudanar da hada hadar cinikayya tsakanin shiyyoyinsu, da ma sauran sassan duniya cikin sauki.
Kaza lika samuwar ababen more rayuwa ya taimaka wajen rage tsadar gudanar da kasuwanci, da bunkasa takarar kasashen Afirka a cikin nahiyar da ma tsakanin su da sauran sassan kasa da kasa, wanda hakan ya haifar da nasarori a fannin raya tattalin arziki da ci gaba mai dorewa.
Wani abun lura ma shi ne yadda kasashen Afirka ke samun karin damar dunkulewa da sauran takwarorinsu, inda hakan ake fatan zai raya burin bunkasa cudanya, da cimma moriyar juna tsakanin kasashen nahiyar da ita kanta kasar Sin nan zuwa shekaru 50 masu zuwa. (Saminu Alhassan)