An kafa MDD ne shekaru 80 da suka gabata yayin da ake cikin burbishin yakin duniya II. Kuma yanzu bayan shekaru 80, duniya tana kan wata muhimmiyar gaba ta shawo kan matsaloli. Sake tasowar yakin cacar baka da amfani da ka’idojin duniya wajen cimma muradu na kashin kai da rashin daidaito ta fuskar ci gaba a duniya, tsarin da ake bi a baya, ba zai iya shawo kan sabbin matsaloli ba.
Bayan shawarwarin raya duniya da ta tabbatar da tsaro da ta wayewar kai, kasar Sin ta sake gabatar da wata mafita, wato shawarar jagorantar harkokin duniya. Wadannan manyan shawarwari 4 sun kunshi cikakken tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, tare da samar da daidaitacciyar alkibla ga duniya mai cike da rashin tabbas. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)













