A ranar 26 ga watan Satumban nan ne ofishin watsa labarai na majalissar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani mai lakabin “Hada kai wajen karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama: Shawara da matakan kasar Sin”. Wannan takardar bayani dai ta zo a gabar da ake cika shekaru goma, tun bayan da shugaban kasar ta Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa, wanda karkashin ta Sin ta gabatarwa duniya da bayanan kwararru, da tsare-tsare na zahiri, da manufofin cimma wannan buri na gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa, domin amfanin bil adama baki daya.
Ga duk wanda ke bibiyar al’amuran rayuwa dan Adam a duniyarmu ta yau, ya kwana da sanin cewa kasashe masu tasowa da dama na ta kokarin koyo daga kasar Sin, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, wadda kuma ta yi nasarar cimma manyan nasarori a bangaren raya kanta, da ma ba da gudummawa ga ci gaban duniya baki daya. A daya bangaren kuma, akwai daidaikun mutane masu tarin yawa daga kasashen yamma, da su ma ke da burin zurfafa fahimtarsu game da kasar Sin, wadanda nazartar wannan takardar bayani zai ba su damar kara saninsu game da mahangar Sin don gane da raya duniya da kowa zai ji dadin zama cikinta.
- Manoman Kenya Na Kara Rungumar Fasahohin Inganta Noma Na Sin
- Kungiyar Kasar Sin Ta Lashe Dukkan Lambobin Zinare Na Wasannin Nutso A Gasar Wasannin Kasashen Asiya
A shekarar 2013, lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara gabatar da shawarar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa, wadda a cikinta ya jaddada cewa, kamata ya yi dukkanin kasashen duniya su kara azama wajen wanzar da zaman lafiya a duniya, tare da hada karfi da karfi wajen wanzar da ci gaban bai daya. Kuma cikin wadannan shekaru goma da suka gabata, harkokin cidanyar kasa da kasa sun gamu da sauye-sauye masu tarin yawa. Cikin mafiya daukar hankali akwai manufofi da wasu kasashen yamma suka bullo da su, ciki har da aniyar “Rabewa da Sin” da “Kebe kai daga Sin”, wadanda dukkaninsu suka sabawa hanyar kyautata yanayin zamantakewar zamanin da muke ciki.
Kaza lika wasu kasashe sun rungumi akidar fito na fito, da rura wutar sabon salon yakin cacar baka, matakin da ke haifar da illa ga hadin gwiwar sassan kasa da kasa. A ’yan shekarun baya bayan nan, sassan kasashe daban daban suna fuskantar zabi mai wahala, na ko dai su amince da tafiya tare da manyan kasashe masu ra’ayin yin fito na fito domin neman riba, ko kuma su zabi hanyar hadin gwiwa da cimma moriya tare, wadda za ta kai ga bunkasa rayuwar al’ummun duniya sama da su biliyan bakwai, da dora duniya kan turba ta gari. Duniya na neman amsoshi, kuma daya daga muhimman amsoshin da ake nema shi ne wannan shawara ta Sin ta gina al’ummar duniya mai maomar bai daya ga kowa.
Ba tare da kambama tasirin shawarar ba, muna iya cewa wannan takardar bayani na kunshe da shawarwari da suka dace da lokacin da ake matukar bukatar su, kuma a wani lokaci mai cike da tarihi. Tun daga taken kundin ma muna iya ganin yadda aka alakanta shawarwarin dake cikin ta ga ci gaban daukacin bil adama baki daya. Kaza lika duk da cewa kasar Sin ce ta gabatar da kundin, shawarwarin dake ciki ba mallakin kasar Sin din ne ita kadai ba. Domin kuwa shawarwarin sun amsa tambayar da aka jima ana yi game da mokamar bil adama, kuma sun zamo tamkar wata muhimmiyar kadara ta daukacin bil Adama baki daya wadda Sin ta gabatarwa duniya.
Kundin bayanan mai kunshe da kusan kalmomi 22,000, ya tabo dukkanin muhimman batutuwa masu ma’ana, cikin harshe mai saukin fahimta, tare da la’akari da abubuwa da dama da suka faru a harkokin kasa da kasa, ta yadda kundin ya samar da taimako ga kasashen duniya ta fannin gabatar da managartan shawarwari na samar da hadin gwiwa mai alfanu ga kowa. Kundin ya gabatar da kira na gudanar da ayyuka a bude, masu hade dukkanin sassa, ta yadda za a samar da duniya mai mai tsafta, mai kayatarwa, mai cike da zaman lafiya, wadda ke da cikakken tsaro, da walwala ga kowa, wadda za ta mayar da mafarkin bil adama na samun kyakkyawar rayuwa ya zama gaskiya.
Sabanin mahangar wasu kasashen yammacin duniya, na tunkarar matsalolin duniya da tunanin “Kwarewar gyara komai” ko “Amfani da dabarun da suka dara na kowa”, shawarwarin dake cikin kundin na Sin sun mayar da hankali ne ga amfani da matakai na adalci da daidaito wajen amfani da dokokin kasa da kasa.
Kawo yanzu, Sin ta yi hadin gwiwar cimma nasarar manufofin gina al’ummar duniya mai makomar bai daya tare da kasashe da yankuna da dama, kana shawarar nan ta bunkasa ci gaban duniya, da shawarar wanzar da tsaron duniya da Sin din ta gabatar dukkaninsu sun samu goyon baya daga kasashe sama da 100, yayin da shawarar wayewar kan duniya ita ma ta samu yabo daga sassa daban daban. Bugu da kari, Sin ta gabatar da shawarwarin warware manyan kalubalolin da duniya ke fuskanta a fannonin kiwon lafiya, da sauyin yanayi, da tsaron yanar gizo da sauran su.
A daya bangaren, shawarar “Ziri daya da hanya daya” ko “The Belt and Road Initiative (BRI)”, ta zamo muhimmin misali na dabarun da kasar Sin ta gabatar domin cimma nasarar kafuwar al’ummar duniya mai makomar bai daya.
Waiwaye Game Da Sassan Kundin Shawarar Ta Sin
Cikin wannan muhimmiyar takarda da kasar Sin ta fitar, mai jigon “Hada kai wajen karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama: Shawara da matakan kasar Sin”, mahukuntan Sin sun bayyana aniyar su ta ci gaba da aiwatar da ayyuka daban daban karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, da nufin haifar da alherai ga kasashen da suka shiga shawarar.
Kaza lika, Sin za ta zuba karin jari, da albarkatun da za su ingiza ci gaban hadin gwiwar duniya, ta yadda hakan zai ingiza burin nan na cimma nasarar ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, tare da ba da sababbin gudummawa na gina duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil adama.
Ko shakka babu wannan takardar bayanai ta nuna hakikanin burin kasar Sin na aiwatar da matakai na hakika, na bunkasa ci gaban kanta, a wani bangare na bunkasa ci gaban al’ummun duniya, ta hanyar gabatarwa duniya sabbin damammaki karkashin sabbin dabarun ta na raya kai.
Masana harkokin cudanyar kasa da kasa na ganin cewa, jam’iyyar Kwaminis mai mulkin kasar Sin na da rawar takawa ta musamman, a fannin bunkasa ci gaban wayewar kan bil adama, da gina duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil adama.
A daya bangaren kuma, kundin ya yi fashin baki game da burin karfafa musayar al’adu tsakanin sassa daban daban a matsayin muhimmin mataki na cimma wannan buri, wanda karkashin hakan, kasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin raya al’adu, da kiyaye al’adun da aka gada daga kaka da kakanni, da raya fannin yawon bude ido tare da kasashen duniya 157.
Cikin sama da shekarun nan 10, kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kasashen duniya masu yawa wajen tsara sama da baje koli 500, masu nasaba da raya musayar al’adu. Alal hakika, cimma burin gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil Adama buri ne mai girma, kuma ko da yake zai haifar da manyan nasarori ga duniya baki daya, ba abu ne da za a cimma nasarar sa a dan kankanen lokaci ba, don haka ya dace dukkanin sassan kasa da kasa su yi hadin gwiwa da juna wajen ingiza nasarar hakan.
La’akari da hakan, idan har ana son cimma nasarar wannan shawara, ya zama wajibi a dora muhimmanci a kuma yi aiki tukuru har a kai ga cimma nasara.
Kasar Sin na fatan sassan kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka, za su kawar da akidun nuna wariya da son kai, maimakon hakan su karkato da tunanin su ga baiwa ci gaban duniya gudummawa. Kaza lika, ya kamata dukkanin kasashen duniya su yi aiki tare karkashin wannan kundin bayanai da Sin ta fitar, ta yadda za a cimma nasarar hade kan duniya, da samar da wadata ta bai daya.
Kafin ma gabatar da wannan takardar bayani ta baya bayan nan, an shigar da shawarar Sin ta gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama shekaru 10 da suka gabata, cikin kudirorin babban zaman majalissar dinkin duniya shekaru Shida a jere, baya ga kudirori, da sanarwar tsarin cudanyar dukkanin sassa, irin su na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, da na kungiyar BRICS. Wadanda tuni suka samu goyon baya daga sassan kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa. To sai dai kuma hakan ya haifar da dar-dar, da turjiya, da ma yunkurin dakile nasara daga wani rukuni na kasashe masu ci gaba kamar Amurka, wadda ta zamo a sahun gaba wajen nuna yatsa ga manufar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya.
Alal hakika, idan da a ce manyan ‘yan siyasar kasashen yammacin duniya sun kawar da ji da kai, sun saurari murya da mahangar kasar Sin, za su gano cewa nasarar wannan shawara ta gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa, ba wai tana da nufin kalubalantar su ba ne, hasali ma al’ummar duniya da ake fatan ginawa, ta hada da al’ummun su, ta fuskar ayyuka da hadin gwiwa, da ingiza bunkasar su kan su kasashe masu wadata. Ba tare da la’akari da girma ko wadatar kasa ba, muna iya cewa, ba wata kasa da za ta ce ta wadatu da wannan manufa mai daraja. Burin dai shi ne bunkasa ci gaban duniya baki daya ba tare da wata wariya ba. Don haka, duk inda wata kasa ko yanki yake a duniya, kama daga masu wadata zuwa masu tasowa, ya zama wajibi su hada karfi da karfe wajen cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da ci gaba mai game kowa da kowa.
Wadanne Karin Matakai Sin Ke Dauka Don Cimma Nasarar Da Aka Sanya Gaba
Daya daga muhimman matakai da Sin ta dauka tun shekaru goma da suka gabata, domin cimma nasarar wannan shawara shi ne gabatar da tsarin ayyukan hadin gwiwa karkashin manufar nan ta “ziri daya da hanya daya” ko BRI a takaice, wanda karkashin ta Sin ta gabatar da budaddiyar shawarar hadin gwiwa mai karko, ta wanzar da hadin gwiwa da kyautata rayuwar al’ummun duniya daban daban.
Bisa alkaluman samar da ci gaba da aka samu daga wannan shawara ta BRI, kamar yadda bankin duniya ya bayyana, idan har an cimma nasarar aiwatar da shawarar BRI yadda ya kamata, cinikayya tsakanin kasashe da yankunan da suka shiga aka dama da su za ta karu da kaso 4.1 bisa dari nan da shekarar 2030, kaza lika shawarar BRI za ta samar da kudaden shiga har dalar Amurka tiriliyan 1.6 a duk shekara.
Wani muhimmin abun lura shi ne shawarar BRI, ta ta’allaka ne da hadin gwiwar raya tattalin arziki, kuma ba ta da wata alaka da siyasar yankuna, ko aiwatar da kawancen soji, shawara ce ta yin tafiya tare a bude, ba tare da mayar da wani bangare saniyar ware ba.
Shawarar BRI wadda ya zuwa watan Yulin shekarar nan ta 2023, ta hallara sama da kaso uku bisa hudu na jimillar kasashen duniya, tare da sama da hukumomin kasa da kasa 30, ba tana nufin kafa wani kawancen Sin na daban ba ne, kana ba kungiyar killace wasu tsirarun sassa ba ce.
A matsayin ta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma mamba a rukunin kasashe dake samun saurin bunkasar tattalin arziki, kasar Sin ta yi namijin kokari wajen tallafawa sauran kasashe masu tasowa, da taimakawa wajen bunkasa ikon kasashen na samun wadata da ci gaba, karkashin manufofi daban daban da shawarwari irin su BRI.
Har ila yau, ta hanyar kulla hadin gwiwa da hukumomin kasa da kasa, Sin ta gudanar da muhimman ayyuka sama da 130 masu nasaba da rage talauci, da samar da isasshen abinci, da dakile sauyin yanayi a kasashe 60, ciki har da Habasha, da Pakistan da Najeriya. Ayyukan da suka amfani sama da mutane miliyan 30.
Takardar ta kara da cewa, shawarar raya kasa ta duniya, da shawarar samar da tsaro ta duniya, da shawarar wayewar kan duniya da kasar Sin ta gabatar, duk sun zama wani muhimmin ginshiki na gina al’ummar duniya mai makomar bai daya.
Kasar Sin ta gabatar da shawarar gina al’ummar duniya mai makomar bai daya, tare da yin kira ga dukkan kasashen duniya, da su samar da kyakkyawar fahimtar juna, da daukar matakan da suka dace, don tinkarar batutuwan da suka shafi duniya, ta yadda za a karfafa gwiwa, da himmatuwa ga yunkurin dan Adam na samun kyakkyawar makoma.
Takardar bayanin ta kara da cewa, bisa zurfin tunani, kasar Sin ta fahimci cewa, mabambantan al’adu suna haifar da sabanin fahimtar yanayin da ake ciki, amma duk da haka, kasar Sin na mutunta kokarin da al’ummun kasashe daban-daban suke yi na nazarin hanyoyin ci gaban da ya dace da yanayinsu.
Yayin da duniya ke fuskantar tarin kalubaloli, wannan takardar bayani ta yi fashin baki filla-filla, wanda ke nuna cewa, kasashen duniya sama da 190 tamkar suna tafiya ne cikin wani jirgin ruwa guda daya. Idan kuwa al’ummar duniya na tafiya ne cikin jirgin ruwa guda, wanda ka iya fuskantar babbar igiyar ruwa, ke nan akwai bukatar dukkanin sassa su ba da gudummawar kare ingancin jirgin ruwa, wanda hakan kare moriyarsu ce ta bai daya.
Kamar yadda wannan takardar bayani ta tabbatar, “Duniya gida ne guda dunkulalle na daukacin bil Adama. Kuma wadanda suka juyawa manufar hadin kan daukacin wannan gida guda baya, ba za su samu wani muhallin rayuwa na daban da za su iya kasancewa a cikin sa ba.”