Sayyada A’isha ta ce, mu da muke Iyalan gidan Manzon Allah (SAW) amma mukan zama wata daya ba mu kunna wutar girki ba sai dai Dabino da Ruwa.
An karba daga Abdurrahman bin Aufin, yana cewa, Annabi (SAW) ya rasu amma da shi da Iyalan Gidansa ba su koshi ba daga Gurasar Sha’ir. Wannan Hadisi ne mai tsawo kuma wanda ya fada wannan Hadisi yana daga cikin masu kudin garin Madina. Ana cewa, da Usman bin Affan da Abdurrahman bin Aufin, kusan rabin kudin duniya, yana hannunsu.
- Yadda Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Suka Gudanar Da Maulidin Manzon Allah (SAW) Na Bana
- Rundunar Sojin Ruwa Ta Kama Kwale-kwale Da Muggan Kwayoyin Miliyan N200 A Legas
Rabon gadon dukiyar Abdulrrahman bin Aufin, abun mamaki ne, wata daga cikin matansa wacce ya rabu da ita da dadewa, sai da aka ba ta Dinari Dubu Tamanin, bayan wasiyyar da ya bari na raba wani kaso na cikin dukiyarshi amma sai da aka bar dukiya mai yawa. Da aka gama rabon dukiyar, sai Sayyadina Usman ya tambayi Sahabbai cewa, me za ku fada game da dukiyar Abdurrahman bin Aufin? Sai Abu Zarrin ya ce, ai wannan wani mutum ne da ya gama cinye Lahirarsa, sai aka tambaye shi, me ya sa za ka fada hakan? Wannan mutum ne Bawan Allah, sai ya ce, mutumin kirki ne zai tara dukiya kamar haka! Abdurrahman bin Aufin, wata rana ya yi Azumi, lokacin bude baki sai aka kawo masa kwanon nau’ukan nama da abinci kala-kala, nan take sai ya tuna rayuwar Manzon Allah (SAW), sai ya fashe da Kuka, ya ce a dauke, “Annabi (SAW) ya rasu bai ci irin wadannan abubuwa ba”. Wannan Tawadu’u ne ya sa ya fadi maganar da muka ambato muku a baya.
Abdurrahman bin Aufin, kasaitaccen mai kudi ne, ya kula da Matan Annabi (SAW) da Sahabbai musammam ‘Yan Badr (Albashi ya ware wa ‘Yan Badr).
An Karbo Hadisi daga Sayyada A’isha da Abi Umamata da Abdullahi bin Abbas suka ce “Manzon Allah (SAW) da shi da Iyalinsa, suna jera Kwanaki ba su samu abincin Dare ba”.
An karbo Hadisi daga Anas bin Malik ya ce “Manzon Allah (SAW) bai taba cin Abinci a kan Teburi ko Filet ba, ba a taba masa gurasa ba wacce aka cire tsakinta ba” – Amma wannan dama ba Al’adar Larabawa ba ce, Turawa da Mutanen Farisa su suke da wannan Al’ada. Anas bin Malik, albarkar Addu’ar Manzon Allah (SAW) akansa, bayan rasuwarsa, da cebur ake diban zinari wajen rabon gadonsa. Al’adar Sahabbai ce ko kuma Muridai, za ka ga kudi ko dukiyar da Allah ya ke mallaka musu, sai ka ga kaman Shehunansu ba su mallaki irin wannan dukiya ba, don haka, in za su ba da labari, sai su ce, Annabi bai ci abinci iri kaza ba.
Anas ya kara da cewa, “ba a taba wa Annabi gurasa wacce aka cire dusarta ba,”. Ma’ana dai, Annabi (SAW) ba mai cin abinci ba ne irin ta koyaushe ba ko kuma ciki-makabarta (komai sai an ci).
An karbi Hadisi daga Sayyada A’isha ta ce “Shimfidar Annabi (SAW) wacce yake kwana a kanta, fata ce jemammiya da aka tsara ta kamar buhu da za a iya dura abu a ciki, Algararar Dabino ce aka dura a cikin fatar”. Ita kuma Sayyada Hafsatu, matar Annabi (SAW), cewa ta yi “Shimfidar Annabi (SAW) ta cikin dakinsa wacce yake bacci a kanta, Bargo ne aka rubanya shi biyu”, wani dare sai muka rubanya shi hudu, yayin da Annabi (SAW) ya wayi gari, sai ya tambaya wacce irin Shimfida aka yi masa, Sayyada Hafsatu ta ce, Shimfidarka ce amma mun rubanya ta hudu, sai Annabi (SAW) ya ce a maida ita yadda take sabida jiya bai samu damar tashin dare ba, taushinsa ya hana ni Sallah”. Manzon Allah ya kasance wani lokaci kuma yana kwanciya a kan gado wanda aka saka shi da igiyar Kaba, har igiyar kabar ta yi zane a jikin kirjinsa.
Sayyada A’isha ta ce, “Cikin Manzon Allah (SAW) bai taba cika ba don koshi”, Malamai suka ce, Sayyada tana nufin cewa, Annabi (SAW) bai taba makare cikinshi da abinci ba irin wanda za ka ga mutum sabida ya ci da yawa da kyar yake numfashi. Annabi (SAW) Balarabe ne, Larabawa suna amfani da Madara, ita kuma Abinci ce mai zaman kanta don haka, tsarin cin abincin Annabi (SAW) ba zai yi daidai da sauran al’ummatai ba. Sa’adu bin Ubadata, shi kadai ya bai wa Annabi (SAW) Rakuma 45 wadanda ya raba wa matansa don tatsar Nono.
“Manzon Allah (SAW) bai taba bayyana bukatarsa ga wani ba sai Ubangijinsa” – Malamai suka yi sharhi da cewa, Annabi (SAW) ba ya roko amma yana da ‘yan sirri, wadanda yake sirri da su. Annabi (SAW) yakan nemi a biya bukatar wasu a wurin sahabbansa amma ba a kanshi ba, don haka, aka rahoto yana cin bashi, har ya rasu Silkensa yana wurin jingina.
Annabi (SAW) ya kasance ya fi son Talauci daga wadata, wannan Tawadu’u ne nasa, kuma bai hana ya koyar da Addu’ar tsira daga Talauci ba inda yake cewa, Talauci ya kusa zama Kafirci, ya bayar da Addu’a cewa, “duk mai karanta ‘Iza waka’ ba zai yi karkaf ba”.
Zuhudun Annabi (SAW), zuhudun mai kudi ne kuma bai dora wa kowa ba, ya ba wa iyalinsa kowacce abincin shekara.
Duk mai son Mushahada da Hadara ko aiki da Aljanu dole sai ransa ta fi jikinsa nauyi, kuma ana iya yin hakan ne ta hanyar takaita ciye-ciye. Idanuwa, jikkuna suke kallo (Basaru), ita kuma Rai, Ruhi take kallo (Basira). Basira ita ce ke kallon abin da ba a gani, don haka, sai rai ta yi Ma’arifa ta yi Ibada ta narke, ta fi karfin jiki, ita ke sarrafa sha’awoyin Dan’adam guda biyar: Gani, Ji, Dandano, Shaka da Shafa. Da irin wannan ne Rai za ta fara ganin abin da ba a gani, har ta koma gani ba da Ido ba, magana ba da baki ba, Shaka ba da Hanci ba, Ji ba da Kunne ba, gane taushi ko taurin abu ba tare da an shafa ba. Annabi (SAW), duk da cewa, shi Annabi ne, Allah ya ba shi duk wannan amma sai da ya dinga shiga Kogon Hira yana Ibada – kogon da aka ce akwai abubuwa masu cutarwa.
Annabi (SAW) ya kasance yakan wuni bai ci abinci ba, haka zai ta juye-juye a kan shimfida sabida yunwa amma hakan ba zai hana shi tashi da Azumi gobe ba.
Amma Alhamdulillah… duk wannan, Annabi (SAW) ya zaba ne sabida kankan da kai ga Allah don haka, ya hana kowa ya yi koyi da shi a wannan bangare.
Sayyada A’isha ta ce, na kasance ina yi wa Annabi (SAW) kuka don jinkai game da halin da nake ganinshi amma haka ya so, wani lokacin har sai na shafa cikinsa sabida halin da cikin ya shiga na daga yunwa, sai na fada masa, raina fansa a gare ka, me ya sa ko abin da za ka ci ba za ka tambaya ba? Tun da ba ka son mai yawa. Sai Annabi (SAW) ya ce min, ya ke A’isha! Wai meye ya hada ni da Duniya ne? Abin da nake tsoro, ‘yan’uwana, Annabawa Ulul’azmi (Annabi Nuhu, Ibrahim, Musa da Isa), ma’abota kokari, sun yi juriya a bisa abin da yafi wannan halin da nake ciki na tsanani kuma suka shude a kan haka, suka tafi wurin Ubangijinsu a haka, Allah ya girmama makomarsu, so kike in je in sami Ubangijina ina jin kunya ban yi komai ba? Sabida ni kawai dan gata ne?