Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce shawarar neman ci gaban kasa da kasa, wani misali ne dake nuna yadda kasar Sin ke ba da gudunmawarta wajen tinkarar matsalolin gudanarwar kasa da kasa, da magance kalubalen da duniya ke fuskanta, wanda ya bayyana ra’ayin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil’adama, da kuma nuna irin nauyin dake kan kasar Sin a fannin diflomasiyya, bisa matsayinta na babbar kasa a sabon zamani.
Wang ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Laraba.
A lokacin da yake amsa tambayar dan jarida game da yadda kasar Sin ke kallon matsayinta, da rawar da take takawa a harkokin duniya, Wang ya kara da cewa, duk yadda yanayin kasa da kasa ya canza, kudurin kasar Sin na aiwatar da tsarin cudanyar bangarori da dama ba zai sauya ba, kuma kokarin da take yi na kyautata harkokin duniya ba zai canza ba, kana ayyukan da take yi na inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban ba zai canza ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)