A baya bayan nan, firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko, ya zanta da kafar CMG ta kasar Sin, inda ya jinjinawa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, wadda ya bayyana a matsayin mai cike da hangen nesa da burikan samar da ci gaba, wanda hakan ya yi daidai da hikima, da managarcin tunanin jagoranci na shugaba Xi Jinping na kasar Sin.
Mista Sonko, ya ce Senegal ce kasar farko a yammacin Afirka da ta karbi wannan shawara. Kuma abu ne mai muhimmanci ganin yadda shawarar ke kara ingiza cimma nasarori ga dukkanin sassan. Sonko ya kara da cewa, cikin ‘yan shekaru kalilan, tarin kasashen Afirka sun cimma manyan nasarori na hakika, daga aiwatar da shawarar.
Ya ce shawarar ba wai ta zo domin sauya alkiblar da daukacin kasashe ke bi ba ne, maimakon hakan, ta samar da zarafi ne na hadin gwiwa dake bayar da dama ga ko wace kasa, ta tattaunawa da Sin gwargwadon moriyar kashin kanta. Mista Sonko ya ce kasashen Afirka na da mabanbantan abubuwa da suke mayar da hankali kan su. Wasu na fatan bunkasa kayayyakin wasanni, wasu na da burin gina manyan hanyoyin mota, da masu fatan bunkasa masana’antu. Kuma Sin na tattaunawa da kasashe daban daban bisa la’akari da hakan, da fatan cimma kololuwar gajiya tare. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp