Baya ga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa da suka amince da shawarar “ziri daya da hanya daya”, a gabar da hankalin duniya ya koma ga taron kolin hadin gwiwar shawarar dake gudana a birnin Beijing na kasar Sin, wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da cibiyar nazarin watsa labaran kasa da kasa a sabon zamani ta tattara, karkashin jagorancin kafar talabijin ta CGTN, dake karkashin rukunin kafofin watsa labarai na kasar Sin CMG, da jami’ar Renmin ta kasar Sin, albarkacin cikar shawarar da kasar Sin ta gabatar shekaru goma cif da kafuwa, matasa dake tsakanin shekaru 18 zuwa 44, wadanda suka bayyana ra’ayinsu, sun amince da tunanin shawarar, da sakamakon da aka samu, tun bayan kafa shawarar shekaru goma da suka gabata zuwa yanzu.
Yayin kada kuri’ar jin ra’ayin jama’ar, an lura cewa, kaso 84.6 cikin 100 na matasan da suka bayyana ra’ayinsu, sun amince da “ruhin hanyar siliki” da kasar Sin ta gabatar, wato “hadin gwiwa cikin lumana, da bude kofa tare da yin hakuri, da koyi da juna, da cin moriyar juna domin samun ci gaba tare” . Bugu da kari, kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ta nuna cewa, matasa masu karancin shekaru sun fi amincewa da shawarar, yayin da kaso 88.8 cikin 100 na matasa masu shekaru 18 zuwa 24, suka amince da “ruhin hanyar siliki”.
- IMF Ta Yi Hasashen Tattalin Arzikin Kasar Sin Zai Karu Da Kaso 5 A Bana
- Kasashe Masu Tasowa Da Abokai Sun Goyi Bayan Matsayin Kasar Sin Mai Adalci A Taron MDD
An gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ce ga matasa 3,857 dake kasashe 35, a kasashen Amurka, da Birtaniya, da Japan, da Afirka ta kudu, da Argentina, da Thailand, da Najeriya, da Peru, da Mexico da sauransu. Baya ga rukunin matasa, shi ma shugaban kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe ya yi nuni da cewa, tun daga farkon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na farko a shekarar 2017 zuwa dandalin tattaunawar na biyu, sannan kuma ya zuwa yau, yanayin duniya ya canja. Musamman, yadda cutar COVID-19 ta yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kowace kasa.
A yayin da duniya ke fama da sabbin matsaloli da manyan kalubaloli, yana fatan samun mafita ta hanyar shiga cikin hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar “ziri daya da hanya daya”. Manufar shawarar “ziri daya da hanya daya” ita ce zamanintar da juna tare, da taimakawa wajen kara karfin kasashe na raya kansu. Daga raba kwarewar ci gaba zuwa horar da kwararru tare, daga bunkasa cinikayyar yanar gizo tsakanin kasa da kasa zuwa tattauna shirin ci gaba, Sin ta kawo sabbin damammaki ga duniya, tare da habaka hanyar zuwa zamanintarwa ta bil’adama. A jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar yayin bude taron hadin gwiwar shawawar karo na uku, ya bayyana cewa, ya dace mu hada kai wajen fuskantar kalubalolin dake gabanmu, ta yadda za a samar da wata makoma mai haske ga ’ya’yanmu da jikokinmu
Duk da cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya” ta samo asali ne daga kasar Sin, amma shawarar ce ta duniya baki daya, kuma ta kawo alheri ga dukkanin bil’adama. (Ibrahim Yaya)