• English
  • Business News
Thursday, October 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Zama Nagge Dadi Goma

by Abdulrazaq Yahuza
2 years ago
Ziri

Kafin fara hadin gwiwa a karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” a tsakanin Kasar Sin da Afirka, kimanin shekara 10 da suka gabata, galibin mutanen Afirka kan kwana su tashi da burin ganin yaushe za su more rayuwarsu irin yadda ‘yan kasashen da suka ci gaba a duniya suke yi.

Idan muka ga ko muka ji labarin kyawawan hanyoyi, tsaftataccen ruwan sha, sufuri mai inganci da sauran ababen more rayuwa a kasashen duniya, abin da ke fitowa daga bakinmu shi ne “wata miyar sai a makota”.

  • Xi Ya Shiryawa Manyan Baki Liyafar Girmamawa
  • Yadda Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Ta Taimaka Wajen Gudanar Da Gasar Cin Kofin Afirka

Amma daga shekarar 2013, yayin da Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, tunaninmu ya fara sauyawa saboda irin ayyukan raya kasa da shawarar ta fara samarwa a kasashen Afirka.

Egypt, na daga kasashen da suka fara rattaba hannu a shawarar ziri daya da hanya daya a 2013 kuma tuni take cin gajiyar lamarin. Akwai gagarumin aikin gina Sabon Babban Birnin Mulki da kuma yankin masana’antu na Suez Canal da zai yi kafada da kafada da takwarorinsa na duniya. Idan aka kammala gina sabon babban birnin zai rage cunkoso a Cairo, babban birnin kasar na yanzu. Kana yankin masana’antun zai kunshi tashoshin jiragen ruwa shida da masana’antu da cibiyoyin kasuwanci daban-daban da kuma gidajen jama’a.

Ita kuwa Nijeriya wacce ta shiga hadin gwiwar shawarar a 2018 kuma har ila yau a bana take cika shekaru 52 da kulla huldar difilomasiyya da kasar Sin, daga cikin ayyukan more rayuwar da ta ci gajiyarsu, akwai shahararren layin dogon nan da aka shimfida a tsakanin Abuja zuwa Kaduna, da na Babban Birnin Tarayya Abuja, da na Legas zuwa Ibadan. Sai sabbin gine-ginen gudanarwa da tarbar fasinjoji da aka samar a manyan filayen jiragen sama na Kano, Abuja, Legas da Fatakwal. Kana ga tashar teku mai zurfi ta Lekki baya ga wasu ayyukan titunan mota da dama.

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Wadannan ayyukan ci gaba sun kawo sauye-sauye masu ma’ana ga rayuwar ‘Yan Nijeriya da dama. Misali, ma’aikatan da ba su da karfin zama a Abuja sun samu saukin zuwa aiki daga Kaduna zuwa Abuja, inda suke zuwa su dawo cikin yini guda.

Haka nan tashar Lekki da ta zama tashar teku mai zurfi mafi girma a Afirka ta Yamma, ana sa rai ta samar da kudin shiga Dala Biliyan 360 da ayyukan yi akalla 170,000.

Bugu da kari, sufurin jiragen kasa da aka kaddamar na cikin Birnin Legas ya taimaka wajen rage cunkoson da ake fama da shi a birnin daga lokacin da aka kaddamar zuwa yanzu, da rage gurbacewar iska a birnin da sauran harkoki na biyan bukatun yau da kullum na ‘yan kasa.

Ba wannan ne ba kadai, akwai sauran ayyuka da dama da Kamfanonin Sin suka gudanar ko suke kan aiwatarwa da ke bayar da gudunmawa ga raya al’umma da tattalin arzikin kasa.

Ba a Nijeriya ne kawai, shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ke sauya rayuwar al’umma ba da tattalin arzikinsu.

A Kasar Uganda, gina babbar hanyar da ta tashi daga Kampala zuwa Entebbe wacce ta zama ta farko a kasar da ake samun kudin shiga da ita, da madatsun ruwa na samar da wutar lantarki a Karuma da Isimba da aikin fadada Filin Jiragen Sama na Entebbe sun saukaka sha’anin sufuri da bunkasa raya biranen kasar da kuma sada ta da sauran takwarorinta na Afirka, kana da ba da gudunmawa ga habakar tattalin arzikinta.

Haka zalika, a sakamakon “Ziri Daya da Hanya Daya”, ‘yan kasar Senegal da ke fama da matsanancin karancin ruwan sha sun ci gajiyar rijiyoyi na zamani 251 da kasar Sin ta gina inda yanzu haka a kalla mutum miliyan biyu ke amfana, baya ga wasu 3,000 da suka samu aikin yi.

A Angola ma, sama da mutum 600,000 sun amfana da aikin jin kai na Kamfanin Layin Dogo na Kasar Sin (CRCC) wanda ya samar musu da ruwan sha na famfo, karon farko a rayuwarsu.

Tabbas, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta zama nagge dadi goma, bisa yadda kasashen duniya akalla 152 (zuwa Janairun 2023), na yankin Turai, Asiya da Afirka suka amince tare da yin hadin gwiwa na ci gaba da Kasar Sin a karkashinta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi
Daga Birnin Sin

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori
Daga Birnin Sin

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan
Daga Birnin Sin

Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan

October 15, 2025
Next Post
Fasinjoji Sun Jikkata Yayin Da Motoci 2 Suka Yi Karo Da Juna A Legas

Fasinjoji Sun Jikkata Yayin Da Motoci 2 Suka Yi Karo Da Juna A Legas

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

Gwamna Lawal Ya Yi Alhinin Kisan Jami’an Tsaro A Zamfara

October 16, 2025
Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

Shugabannin Kasashe Da Dama Sun Yaba Wa Sin Kan Gudummawar Da Ta Bayar A Fannin Tabbatar Da Daidaiton Jinsi

October 16, 2025
Sabbin Ministoci

Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin Shugaban INEC

October 16, 2025
Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

Ɗaga Matsayin Dangantakar Zambia Da Sin Ya Haifar Da Manyan Nasarori

October 16, 2025
Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zaman Kurkuku

October 16, 2025
Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Amupitan Ya Isa Majalisar Dattawa Domin Tantance Shi A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

Majalisar Dattawa Ta Fara Tantance Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC

October 16, 2025
An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

An Dakatar Da Tashi Da Saukar Jirage A Kenya Don Karɓar Gawar Raila Odinga

October 16, 2025
Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

Gwamnan Edo Ya Umarci Kwamishinoni Su Riƙa Sanya Hular Tinubu

October 16, 2025
Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

Baba-Ahmed Ya Zargi El-Rufai Da APC Kan Haifar Da Rashin Tsaro Don Neman Mulki

October 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.