Mai Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a lokacin da yake karbar gaisuwar barka da sallah a garin Daura, ya bayyana cewa ya kagara wa’adin mulkisa ya cika ya sauka, kana daya daga cikin dattawan kasa, ya ka fahimci wannan maganar?
To, magana ce wadda manya ba sa yin irin ta, domin duk wanda yake da nauyin jama’a a kai bai kamata ya fadi haka a bainar jama’a ba ko kuma masu magana da yawunsa su maimaita wa jama’a ita ba, cewa shugaban kasa ya gaji har ma ya kosa ya sauka daga kan karagar mulki. To idan shi ya gaji a matsayinsa na shugaban kasa duk abin da yake nema za a yi masa, to talakawa ya za su ce game da kashe-kashe da sace-sace, in dai Shugaban Buhari zai ce mulki ya ishe shi har ma ya ji ya kosa ya sauka? Ko haka din ne ma, shugaba ba ya irin wannan magana, domin daurewa ake yi ko da gaske ya gajin, ba dole sai ya tsaya har lokacin wa’adinsa ya yi ba.
Ba wahayi ba ne a ce dole Shugaban Kasa Buhari ya cika wa’adin mulkinsa wanda zai kare a ranar 29 ga watan Mayun 2023 sannan ya sauka. Amma muna cikin wannan hali, muna neman yadda zai ce mana a yi hakuri za a kara kokari, amma sai ya ce ya gaji, ai manya ba sa irin wannan magana. Idan ya gaji ne ko kuma ba zai iya ba, sai ya ce gaskiya na yi iyakan kokarina amma na gaza, bari in bai wa wani, a ji tsoron Allah haka, haka ake gudanar da shugabanci.
Ba ku ganin cewa wata kila wasu ne suka hura masa wuta ko suka matsa masa lamba, duk da cewa yana iya bakin kokarinsa wurin shawo kan matsaloli da kasar ke fuskanta, ba ku ganin cewa wasu ne ke gallaza masa har ya furta haka?
To, mu dai ‘yan jarida ne suka fada mana cewa ya yi wannan magana, a lokacin da ya yi wannan magana akwai gwamnoni na jam’iyyarsa tare da masu magana da yawunsa irin su Garba Shehu. Ai ka ga ba za ka ce akwai mutanen da suka sa masa bakin bindiga har ya furta wannan maganar ba. Idan kana nufin matsalolin ne suka ishe shi, idan kuma matsala ce ta ishe ka har ka kosa ka sauka daga kan karagar mulki, to mene ne amfanin ka ce ba za ka sauka ba sai bayan wata takwas. Idan yana so ne ya ce ya gaji ko ya kasa, to wanda ya gaji ko ya kasa ba ya iya mulki, domin daukar nauyin jama’a ba karamin abu ba ne, ko a nan duniya jama’a ba su yi maka shari’a ba akwai shari’ar lahira, mulki ba karamin abu ba ne, domin ba ka karbarsa idan ka san ba za ka iya ba. Idan kuma ka amsa ka kai wani wurin da ba za ka iya ba, sai ka ajiye. Ko ma dai mene ne, mu dai a bakinsa muka ji, domin shi mai fada a ji ne.
Akwai wadanda za su fahimci kamar shugaban yana kankan da kai ne wato tawali’u, shi ya sa har ya furta wannan magana, domin kar a zaci ko yana da wani shiri na neman karin wa’adin mulki…
To mu ba mu ga wannan alamar ba. Babu tawali’un da ya fi inganci kamar shugaban da yake shugabanci ya ga ba zai iya ba ko ya kai makura ba zai iya ci gaba ba ko kuma ba ya da maganin matsalolin da suka addabi wadanda yake shugabanci, sai ya ce ku nemi wani ya ci gaba da wannan aiki. Idan liman na sallah alolarsa ta karye, sai ya jawo wani daga sahun baya ya ci gaba da sallah. Ba a wasa da mulkin jama’a, sannan kuma ba a wasa da shugabanci, domin idan ba a damu da duniya ba, to a tuna da lahira ranar da za ka tsaya gaban Allah ya yi maka hisabi ya tambayeka a kan ka nemi mulki na ba ka, sannan lokacin da ake abubawa a karkashin mulkinka da sanin ka da ranka da lafiyarka me ka yi. Sai aka ce ai Allah na gaji ne a lokacin ko ka ce abun ya ishe ni ko gidanka ne akwai lokacin da ‘ya’yanka ma idan shekaru suka zo ko rashin lafiya sai ka kasa tafiyar da gidanka ballantana kasa baki daya.
A matsayinku na Kungiyar Dattawan Krewa ta NEF, tun da ya fadi wannan maganar kun dan yi wata hoffasa ganin cewa dan yankinku ne, wajen nuna masa cewa wannan maganar da ya fada ba ta dace ba?
Ina tsammanin ba maganar dan yankin ba ne, kila ko a cikin gidan Shugaban Kasa Buhari mutane daidai ne wadanda za su iya zama da shi su fada masa cewa a nan ka yi daidai, nan ba ka yi daidai ba, ga alamar da muke gani. Mu dai ba mu da wannan hanya ko wannan fadar da za mu je wurin Shugaban Kasa Buhari mu ce masa ka yi kuskure, ko da manya sun gaza ba sa fadi. Idan kuma da gaske din sun gaza, ba za su fadin irin wannan kalamai ba, domin mu ya dade da rufe mana kofa, kuma wannan maganar ya riga ya yi ta har ‘yan jarida sun bayyana ta, sannan a wurin da ya yi wanna magana daga shugaban kasa sai gwamnoni da masu magana da yawunsa irin su Garba Shehu kuma babu wanda ya sa masa wannan kalami a bakinsa shi ya fadi abun sa. Sai dai a koma daga baya a ce ya yi kuskure ko kuma bai fadi daidai ba, amma har yanzu babu wanda ya fito ya ce karya ake masa ko sharri ake masa.
Misali, yanzu da a ce mai girma shugaban kasa zai karanta wannan hirar, wani sako ne za ka isar a gare shi game da wannan batun, wata shawara za ka ba shi kai-tsaye?
Zan ba shi shawara cewa a matsayinsa na Musulmi ya ji tsoron Allah, ya tuna akwai ranar hisabi, ranar da Ubangiji zai tambaye shi. Idan mulkin kasar nan ya zama mishi matsala ko ya kasa ko yana ganin babu wata hanyar da zai bullo ko ma dai laifin ma wane ne, amma duk gaba daya kowa a karkashinsa yake kuma ba zai iya magance wa jama’a matsalolin da ya addabe su ba, to ya ajiye mulkin nan domin ba kai daya ka fara ba kuma ba abin kunya ba ne. Ka rage wa kanka fitinar duniya da lahira. Idan kuma da gaske ba ka gaji ba ne, kana da sauran abin da za ka iya kara tabukawa, to ka kara daura damara ka yi, amma ka daina gaya wa mutane cewa kai abin ya ishe ka har ma yanzu ka fara kosawa ka koma gida, domin kana kara karya wa mutane zuciya ne. To kai ma kenan ka gaji balle mu da muke fuskantar yau a kashe mutane a nan, jibi a sace a can, to sai jama’a su ce me? Abin da zan fada masa kenan.
…Ba Ni Na Tsayar Da Kanena Datti Mataimakin Obi Ba, In Ji Shi
A wani labarin kuma, mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya ce ba shi da hannu a batun tsayar da kanensa, Datti Baba-Ahmed a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Mista Peter Obi ba.
Ya bayyana haka ne a shafinsa na ‘Facebook’ da aka tabbatar nasa ne a daren ranar Laraba.
A bayanin da ya yi, Dakta Hakeem ya fara da bayyana cewa, “Na tsai da shawarar in yi bayani takaitacciya a kan takarar da kanina, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya fito a matsayin mataimakin Mista Peter Obi, dan takarar Shugaban kasa a jamiyyar Labour Party.Mutane da yawa sun tuntube ni su ji bayani, musanman ko ina da hannu wajen shigar Datti wannan takara, ko kuma akwai gaskiya a kan karerayin da Mahadi Shehu ya yi musu cewa da ni da Farfesa Ango Abdullahi, mun karbi tallan Mista Peter Obi daga hannun tsohon shugaban kasa, Obasanjo.
“Datti kanena ne, kuma ya dade yana siyasa.Duk wani abin da ya shafe shi muhimmi, yakan shaida mini, ko ya nemi shawara.Ni kuma nakan ba shi shawarwari, wani lokaci ko bai tambaya ba.Shi ba yaro ba ne. Mutum ne wanda ya mallaki hankalinsa, kuma idan na ba shi shawara, ba abin da zan je ina shaidawa a bainar jama’a ba ne. A kullum kuma ina masa fatan Allah ya sa alheri a abubuwan da ya sa a gaba. Shigarsa Labour Party da karban mukamin mataimakin Peter Obi ra’ayinsa ne, kamar na kowa wanda yake da ‘yancin shiga siyasar da yake so.
“Ban da aikina na Maimagana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa, ni cikakken dan jam’iyyar PRP ne, kuma na shiga jam’iyyar ne da niyyar taimakawa, mu ginata ta zama mana alheri a Arewa da Nijeriya. Nawa ra’ayin ke nan.
“Alhamdu lillahi, na gode wa Allah da ya ba ni dama na bauta masa, kuma in ba da gudummuwa ta wajen gyara zamantakewar mu ‘yan Arewa a Nijeriya. A halin da nike a yanzu, babu wanda zai ba ni wani abu, ko ya tursasa ni in yi abin da na san zai bata mini rayuwata, ko ta jama’ar da nake wa hankoro, ko bayan rayuwata. Ina kuma fata Allah ya dauki raina a cikin wannan halin.
“Na san akwai wadanda suka damu saboda ba su san gaskiyar magana ba.Wasu kuma ba su so Datti ya yi takarar da ya shiga ba.Wasu kuma sunji maganganu marasa dadi sun yi watsi da su. Kamar kullum, na yafe wa dukkan wanda ya yi mini zargi babu hujja, ko cikin rashin sani. Irin zamanin da muke ciki ke nan.Babu wata hujjan yin wannan bayanin illa in faiyace wa wadanda suke bukata su ji gaskiyar magana.Wanda kuma ya ji, bai yarda ba, ruwansa.” Kamar yadda sanarwar ta sa ta bayyana.