• Leadership Hausa
Monday, January 30, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa Ya Tsere Daga Kasar

by Sadiq
7 months ago
in Labarai
0
Shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa Ya Tsere Daga Kasar

Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga kasar Sri Lanka a jirgi sama na yaki, a yayin da ake ci gaba da zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ke fama da shi.

Rundunar sojin sama ta kasar ta tabbatar da cewa shugaban kasar, mai shekara 73, ya tsere zuwa Maldives tare da matarsa da jami’an tsaro biyu.

  • An Tsinci Gawar Jarumin Fina-Finan Nollywood, Abuchi Ikpo A Gidansa
  • Na Matsu Mulkina Ya Kare Na Sauka – Buhari

Sun isa babban birnin kasar, Male, da misalin karfe 3 na dare, kamar yadda rahotanni suka rawaito.

Tserewar da shugaba Rajapaksa ya yi daga kasar ta kawo karshen mulkin da iyalansa suka kwashe fiye da shekaru 20 suna yi a kasar Sri Lanka.

Shugaban kasar ya buya bayan da dandazon jama’ar da ke zanga-zanga suka mamaye gidansa a ranar Asabar, kuma ya yi alkawarin sauka daga mulki a ranar Laraba, 13 ga watan Yuli.

Labarai Masu Nasaba

DSS Ta Kama Wasu Ma’aikatan Banki Masu Hada-hadar Sayar Da Sabbin Kudaden Naira

Tsohon Firaministan Kenya, Odinga, Ya Iso Nijeriya Don Halartar Taron LEADERSHIP Na 14

Wata majiya ta bayyana cewa Rajapaksa ba zai ci gaba da zama a Maldives ba don haka yana da niyyar zuwa wata kasar.

Dan uwansa, wanda shi ne tsohon Ministan Kudin kasar Basil Rajapaksa, shi ma ya tsere daga Sri Lanka kuma an ce ya nufi Amurka.

A yayin da ‘yan kasar Sri Lanka suka wayi gari da labarin tserewar shugaban kasar, dubban mutane sun bazama kan titunan Colombo, babban birnin kasar.

Da dama daga cikinsu sun taru a Galle Face Green, babban filin da ake gudanar da zanga-zanga a kasar.

Tags: Sri LankaTsadar RayuwaTserewaZanga-zanga
Previous Post

An Tsinci Gawar Jarumin Fina-Finan Nollywood, Abuchi Ikpo A Gidansa

Next Post

Da Dumi-Dumi: Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Sakamakon Rushewar Gini A Legas

Related

DSS Ta Kama Wasu Ma’aikatan Banki Masu Hada-hadar Sayar Da Sabbin Kudaden Naira
Labarai

3 hours ago
Tsohon Firaministan Kenya, Odinga, Ya Iso Nijeriya Don Halartar Taron LEADERSHIP Na 14
Labarai

Tsohon Firaministan Kenya, Odinga, Ya Iso Nijeriya Don Halartar Taron LEADERSHIP Na 14

4 hours ago
Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Ya Dawo Aikin Jigilar Fasinjojinsa Bayan Hatsarin Da Ya Yi

2023: Laifin Me Na Yi Wa Mutanen Da Suke Cin Amana Ta —Tinubu

7 hours ago
Gwamnatin Kano Ta Shirya Tarbar Zuwan Buhari Kano Bayan Kara Wa’adin Daina Tsaffin Kudi

9 hours ago
Buhari Ya Nada Dogara A Matsayin Sabon Darakta Janar Na Hukumar NYSC

20 hours ago
Next Post
Da Dumi-Dumi: Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Sakamakon Rushewar Gini A Legas

Da Dumi-Dumi: Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Sakamakon Rushewar Gini A Legas

LABARAI MASU NASABA

Gogewar Kasar Sin A Fannonin Ilimi Da Binciken Kimiyya, Abun Karfafa Gwiwa Ne Ga Kasashen Larabawa 

January 30, 2023
Babban Kwamatin Ayyuka Na Jam’iyyar PDP Na kasa Ya Gana Da ‘Yan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar

‘Yan Majalisar Tarayya 3 Na Jam’iyyar APC Sun Koma Jam’iyyar PDP A Jihar Katsina

January 30, 2023
Kasar Sin Ta Tsawaita Wasu Dabarunta Na Kudi

Kasar Sin Ta Tsawaita Wasu Dabarunta Na Kudi

January 30, 2023
DSS Ta Kama Wasu Ma’aikatan Banki Masu Hada-hadar Sayar Da Sabbin Kudaden Naira

DSS Ta Kama Wasu Ma’aikatan Banki Masu Hada-hadar Sayar Da Sabbin Kudaden Naira

January 30, 2023
Tsohon Firaministan Kenya, Odinga, Ya Iso Nijeriya Don Halartar Taron LEADERSHIP Na 14

Tsohon Firaministan Kenya, Odinga, Ya Iso Nijeriya Don Halartar Taron LEADERSHIP Na 14

January 30, 2023
Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Ya Dawo Aikin Jigilar Fasinjojinsa Bayan Hatsarin Da Ya Yi

Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Ya Dawo Aikin Jigilar Fasinjojinsa Bayan Hatsarin Da Ya Yi

January 30, 2023
Tinubu Ya Godewa Buhari Kan Amincewa Da Kara Wa’adin Kwanakin Daina Karbar Tsoffin Kudade

Tinubu Ya Godewa Buhari Kan Amincewa Da Kara Wa’adin Kwanakin Daina Karbar Tsoffin Kudade

January 30, 2023
2023: Laifin Me Na Yi Wa Mutanen Da Suke Cin Amana Ta —Tinubu

2023: Laifin Me Na Yi Wa Mutanen Da Suke Cin Amana Ta —Tinubu

January 30, 2023
Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano Ta Cafke Jarumar TikTok Murja Ibrahim Kunya

Ina Addu’ar Allah Ya Saukar Min Da Cutar Da Za Ta Sa Na Shiryu – Murja Ibrahim Kunya

January 30, 2023
Gwamnatin Kano Ta Shirya Tarbar Zuwan Buhari Kano Bayan Kara Wa’adin Daina Tsaffin Kudi

Gwamnatin Kano Ta Shirya Tarbar Zuwan Buhari Kano Bayan Kara Wa’adin Daina Tsaffin Kudi

January 30, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci