Da yammacin jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari tare da shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas, inda shugabannin biyu suka bayyana kafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa, bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Falasdinu, kana shugaban Sin ya gabatar da shawarwari guda 3, don warware batun Falasdinu, wannan ya shaida cewa Sin na goyon bayan Palesdinawa wajen mayar da hakkinsu na al’umma, da gabatar da taswirar warware batun Palesdinu baki daya.
Idan aka kwatanta da yarjejeniyar da tsohuwar gwamnatin Trump ta kasar Amurka ta gabatar a shekarar 2020, shawarwarin Sin sun nuna girmamawa, da kare kudurin MDD kan wannan batu.
Kana kasar Sin ta jaddada cewa, ya kamata a tabbatar da bukatun Palesdinu a fannonin tattalin arziki da zaman rayuwar jama’a, kana sassan kasa da kasa su kara samar da gudummawa wajen bunkasa kasar, da kuma tabbatar da jin kai a kasar.
Ban da wannan kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, ya kamata a kiyaye yin shawarwari cikin lumana don warware batun, a matsayin hanya daya tilo ta warware batun.
Kamar yadda mujallar “The Diplomat” ta kasar Amurka ta yi sharhi, Sin ta kasance “Bangaren ba ruwanmu” na hakika. (Zainab)