Bayan kammala tarukan da tawagogin kasashen Sin da na Amurka suka gudanar game da batutuwan raya tattalin arziki da cinikayya a ranakun 10 da 11 ga watan nan na Mayu a birnin Geneva na kasar Switzerland, masharhanta sun bayyana kyakkyawan fatan shawo kan manyan sabani da sassan biyu suke fuskanta, wadanda suka haifar da koma baya ta fuskoki daban daban ga su kansu kasashen biyu, da ma sauran kasashen duniya baki daya. Ko shakka babu sassan biyu sun kai ga cimma nasara ne sakamakon yadda suka zurfafa musaya da shawarwari bisa sahihanci.
Cikin muhimman nasarorin da aka kai ga cimmawa akwai jingine haraji daban daban da sassan biyu suka kakabawa juna, tare da amincewa a ci gaba da tattaunawa a nan gaba domin kaiwa ga wata matsaya mai dorewa. Har ila yau, sun amince da kafa tsarin tuntuba domin nan gaba, wanda zai mayar da hankali ga tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayya dake janyo hankulansu. Kuma da haka, ma iya cewa an kai ga cimma nasarar kafa muhimmin mataki na warware bambance-bambance ta hanyar shawarwari da tattaunawa, tare da kafa tubalin samar da kyakkyawan yanayin ci gaba, da warware sabani da zurfafa hadin gwiwa.
- Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa
- NNPP Ta Tafka Asara, Ƴan Majalisa 2 Daga Kano Sun Koma APC
Alal hakika, duniya ta gamsu da wannan sakamako mai gamsarwa, duk da dai akwai bukatar dorewarsa domin cimma cikakkiyar nasara, wadda za ta ingiza ci gaban tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu da ma duniya baki daya.
Kamar dai yadda ta bayyana bayanan karkare zaman da aka gudanar, sassan biyu sun yi amanna da muhimmancin alakar tattalin arziki da cinikayyarsu, da ma muhimmancin dorewar hakan domin cimma moriyar bai daya cikin lumana.
Duk da cewa aikin da za a fuskanta nan gaba na da matukar muhimmanci, kuma mai yiwuwa yana tattare da kalubale, a bangarenta kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Amurka, wajen wanzar da ruhin wannan tattaunawa. Idan har an yi aiki da sahihiyar zuciya wajen warware matsalolin da aka sanya gaba, ba shakka Sin za ta ci gaba da cika alkawuran da ta dauka, tare da raba ribar ci gabanta da sauran sassan duniya kamar dai yadda ta alkawarta, kuma take aiwatarwa tun tuni.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp