• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shehu Sani Ya Buƙaci Shugabannin Arewa Su Mara Wa Tinubu Baya Ya Yi Shekaru 8 A Kan Mulki

by Sadiq
5 months ago
Sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya soki shugabannin Arewa bisa gazawar da suka yi wajen bunƙasa yankin, inda ya ce lokaci ya yi da za su nemi gafara kuma su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya kammala shekaru takwas a mulki.

Yayin da yake magana da manema labarai a gidansa a ranar Litinin, Sani ya ce Arewa ta samu ci gaba a zahiri cikin shekaru biyu kacal na mulkin Tinubu.

  • Jiragen Yakin NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 20, ‘Yan Banga 2 A Zamfara
  • Shettima: Shekaru Biyu Na Mataimaki, Jagora Mai Hangen Nesa Da Kawo Sauyi Nagari

Ya ce, “Wasu daga cikin shugabanninmu sun samu dama su inganta rayuwar al’ummar Arewa amma sun kasa. Ya kamata su nemi afuwa. Yanzu da muna da gwamnati da ke aiki yadda ya kamata, wajibi ne mu ba ta goyon baya.”

Sanata Sani ya kuma gargaɗi mutanen Arewa da ka da su bari siyasar ƙabilanci ta raba su da gwamnatin da ke aiki fiye da na baya, yana mai tuna musu cewa Tinubu ya mara wa shugabannin Arewa baya lokacin da suke mulki.

Ya jaddada cewa yankin Arewa maso Yamma ya fitar da shugabanni biyu tun daga 1999, Umaru Musa Yar’Adua da Muhammadu Buhari kuma yankin Kudu maso Yamma ya mara musu baya ba tare da wata matsala ba.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa.

Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.”

Sanatan ya kuma soki gwamnatin baya da cewa ko da yake kusan dukkan shugabannin tsaro sun fito ne daga Arewa, amma hakan bai dakatar da ta’addanci a yankin ba, kuma bai hana hare-hare da kashe-kashe a jihohin Filato, Binuwai da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu
Manyan Labarai

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025
Next Post
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Ondo Da Shugaban Masu Rinjaye Sun Yi Murabus

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Ondo Da Shugaban Masu Rinjaye Sun Yi Murabus

LABARAI MASU NASABA

Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

Kasar Sin Ta Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-biyar Na 15

October 25, 2025
Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu

October 25, 2025
An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

An Kaddamar Da Nuna Muhimman Shirye-shiryen CMG A Membobin APEC

October 25, 2025
Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.