Ranar 22 ga watan Sha’aban, Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya cika shekaru 40 da jagorancin Masallacin Harami.
Sallarsa ta farko ita ce a ranar 22 ga watan Sha’aban 1404 a lokacin yana dan shekara 22 kacal, kuma shi ne limami mafi karancin shekaru da ya ja sallah a tarihin Masjidul Harami.
- Hatsarin Mota Sun Yi Ajalin Mutum 17, 17 Sun Jikkata A Bauchi
- Zaben Gwamnoni: INEC Ta Gargadi Jam’iyyun Siyasa Kan Tada Tarzoma
Sudais ya ci gaba da zama mashahurin mai karatu a duniya kuma sananne ga dukkan Musulmi daga ko ina duniya.
Ya shafe shekaru arba’in yana hidima a Masallacin Harami.
Muna rokon Allah Ya albarkaci rayuwarsa, Ya amfanar da Musulunci da Musulmi ta hanyarsa, Ya saka masa da mafificin alheri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp