A cikin sarkakiyar yanayin siyasar kasa da kasa, da jerin kalubalen da ke fuskantar bil’Adam wandada ba kasafai za a shawo kansu ba, akwai kyakkyawar fata da kuma ci gaba yayin da muka shigo cikin shekarar 2024. Duk da rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya, da gwagwarmayar shugabancin duniya tsakanin kasashen yamma da sauran kasashen duniya, da rikice-rikicen sauyin yanayi, da sauran batutuwan da suka mamaye kanun labarai a shekarar 2023, yana da muhimmanci mu waiwayi ci gaban da bil’Adama suka samu ta hanyar hadin kai, da ci gaban sabbin fasahohi musamman na zamani, da yunkurin diflomasiyya, da binciken sararin samaniya, wadanda suka ba da gudummawa ga kyakkyawar labarin ci gaba da burin bai daya na bil’Adama a shekarar bara, shi ya sa muke kyautata zaton shigowa shekarar 2024 da kafar dama.
Cudanya da mu’amala da muke yi da juna suna ba da damammaki ga hadin gwiwa, da fahimta, da warware matsaloli na gama gari. Ta hanyar mai da hankali kan wadannan abubuwa masu kyau, za mu iya yin aiki don gina makomar da ke nuna mafi kyawun damammaki ga bil’Adam, wato makomar da ke da alaka da hadin kai, kirkira da sadaukar da kai ga raya zamantakewar al’ummarmu.
- Burin Sin Na Kara Jin Dadin Zaman Jama’a Ya Dace Da Begen Jama’ar Kasa Da Kasa
- Xi Da Kim Sun Ayyana Shekarar 2024 A Matsayin Shekarar Abokantaka Tsakanin Sin Da Koriya Ta Arewa
An samu munanan rikice-rikice na kasa da kasa da suka barke a cikin 2023, daga yakin da aka dade ana tafkawa tsakanin Rasha da Ukraine zuwa rikicin baya-bayan nan a zirin Gaza, ba sai na ambato yawan tsokanar da Amurka ke yi a tekun kudancin kasar Sin ba, wadanda suka haifar da a kalla illoli guda biyu masu lahani ga tattalin arzikin duniya. Na farkon ya zo daidai da yunkurin da Amurka ke yi na bata tsarin samar da kayayyaki a duniya ta hanyar amfani da jadawalin kudin fito, da haraji, da takunkumi. Na biyun shi ne sakamakon zagon kasar da Amurka ke yi da na ambato, ya haifar da wani sabon yakin cacar baki, wanda ke da illa ga ci gaban tattalin arzikin duniya da kuma jin dadin rayuwar bil’Adam tare da makomar bai daya.
A taron kolin tattalin arzikin kasar Sin da aka gudanar a ranakun 11 da 12 ga watar Disamban shekarar da ta shude a nan birnin Beijing, shugabannin kasar Sin su yanke shawarwari kan muhimman batutuwan da suka shafi harkokin tattalin arziki a shekarar 2024. A gun taron, an bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu farfadowa, tare da samun ci gaba mai inganci. A dunkule, yanayi mai kyau ya zarce kalubaloli game da ci gaban kasar Sin, kuma tushen tsarin farfado da tattalin arziki da kyakkyawan hangen nesa na dogon lokaci bai canza ba.
A duk halin da ake ciki dai, kasar Sin za ta yi iya kokarinta wajen samar da tsare-tsare da kuma tuntuba da tattaunawa domin kara fahimtar muradun bai daya. Ba za ta nemi kasashen duniya da su rarrabu ba, akasin haka, za ta kiyaye ingancin tsarin samar da kayayyaki na duniya da sunan kyautata jin dadin jama’a kan karin kariyar ga kasashen duniya.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekara ya ce, “al’ummar Sinawa na dora matukar muhimmanci ga zaman lafiya. Muna fatan za mu hada kai da daukacin kasashen duniya. Ya kamata mu yi la’akari da makoma da jin dadin bil’Adam. Ya kamata mu kara azama kan raya kyakkyawar makomar bai daya ta bil’Adama da gina duniyarmu da kowa zai ji dadin zama a cikinta”. (Yahaya)