A wadannan kwanaki, Sinawa suna murnar bikin sabuwar shekara ta gargajiyarsu, wanda ake kira “bikin bazara”. Don taya murnar bikin, wani abokina dake Kano ya buga mana waya a jiya. Ya fahimci al’adun kasar Sin sosai, don haka ya san Sinawa na yin amfani da zagayowar wasu dabbobi 12, wajen wakiltar shekaru daban daban. Ya ce mana: “Ina taya Sinawa murnar sabuwar shekara ta Zomo, da fatan kowa zai kasance cikin koshin lafiya, da iya gudu cikin sauri, kamar yadda zomo yake.”
Ina godiya sosai bisa fatan alheri da aka yi mana, kana na ga wasu abubuwa suna “gudu cikin sauri” a nan kasar Sin, kamar dai yadda wannan aboki ya fada.
Da farko, annobar COVID-19 nau’in Omicron na “gudu”, inda ake sa ran ganin bayanta cikin sauri a nan kasar Sin.
Bisa alkaluman da cibiyar kandagarkin cututtuka ta kasar Sin ta bayar, an ce an samu mafi yawan mutanen da suka nemi samun jinya a asibiti a kewayen ranar 22 ga watan Disamban bara, inda yawansu ya kai miliyan 2 da dubu 867 a duk rana. Daga baya jimillar ta fara raguwa. Zuwa ranar 23 ga watan da muke ciki, jimillar ta sauka zuwa dubu 110, wato ta ragu da kashi 96.2%.
Kar mu manta, ana samun mafi yawan zirga-zirgar mutane a lokacin bikin bazara a kasar Sin, musamman ma ta la’akari da yadda kasar ta sassauta matakan kandagarkin yaduwar cutar COVID tun daga karshen bara, inda ko a ranar 24 ga wata kadai, aka samu fasinjoji fiye da miliyan 29 da suka yi zirga-zirga a kasar, adadin da ya karu da kashi 67.3% bisa makamancin lokacin bara. Amma duk da haka, kwararar mutane ba ta tsananta yanayin bazuwar COVID ba. Hakan ya nuna cewa, matakan hana yaduwar annoba da aka daidaita su, sun yi amfani.
Na biyu shi ne, bayan da yanayin annoba ya yi sauki, tattalin arziki ma na farfadowa cikin karin sauri.
A wadannan kwanaki, na ziyarci cibiyoyin kasuwanci na Beijing, da wuraren cin abinci, da kallon sinima, da sauran nune-nune, inda na ga ko ina na cike da mutane, kana suna kokarin sayayya da kashe kudi. Alkaluman da hukumar kasuwanci ta birnin Beijing ta gabatar sun nuna cewa, daga ranar 21 zuwa ta 24 ga wata, wato cikin kwanaki 4 kacal, darajar kayayyaki da abinci da aka sayar da su a birnin Beijing ta kai Yuan biliyan 2.84, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 420.
Kana wannan yanayi mai armashi ya bazu a wurare daban daban. Bisa abun da na gani a telabijin, a duk wani gari na kasar Sin, ana samun cunkuson mutane a wuraren shakatawa, inda ‘yan kasuwa ke shan aiki, suna farin ciki bisa dimbin ribar da suka samu. To, yadda aka samu farawar sabuwar shekara kamar haka, ya nuna yadda tattalin arzikin kasar zai samu ci gaba cikin karin sauri a wannan shekarar da muke ciki.
Har yanzu ban manta da bikin bazara na shekaru 3 da suka wuce ba. Inda a ranar 23 ga watan Janairun shekarar 2020, birnin Wuhan da aka samu barkewar annobar COVID-19 a cikin sa, ya sanar da killace kansa, kana wurare daban daban na kasar Sin suka fara tura mutane da kayayyakin da ake bukata zuwa birnin don ba shi taimako. A lokacin, na soke shirin ziyara, inda ni da iyali na muka kasance a gida don magance kamuwa da cuta.
Sa’an nan a shekaru 2 da suka biyo baya, an ci gaba da daukar tsauraran matakan kandagarkin cuta a nan kasar Sin. Inda mutanen kasar suka yi kokarin hana yaduwar cutar COVID-19, bisa hadin gwiwa, da da’a, da jajircewa, don kare rayukan jama’a daga mummunar cutar mai kisa. Ana ci gaba da wannan kokari, har zuwa karshen shekarar bara, lokacin da aka samu cikar sharudan sassauta matakan kandagarkin cuta.
Saboda haka a wannan bikin bazara, Sinawa sun samu cikakkiyar damar jin dadin haduwa da iyalai, da ziyara a wurare daban daban. Sai dai an fi samun sauyawa cikin zukatansu, inda tsoron kamuwa da cuta ya ragu sosai, kana imani game da makoma mai haske ya karfafa.
Burina shi ne, wannan imani na Sinawa zai taimakawa karfafa gwiwar mutanen kasashe daban daban, kana ci gaban tattalin arzikin Sin zai sa tattalin arzikin duniya samun farfadowa cikin matukar sauri, har ma ya fi saurin gudu na zomo, a wannan shekara ta zomo da muke ciki. (Bello Wang)