Tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya bukaci Shugaban kasa, Bola Tinubu ya rage yawan ministocinsa, domin rage kasha-kashen kadaden gwamnati.
Shekarau ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin din Channels a ranar Talata.
- Mutum Dubu 29 Sun Nemi Aikin Dan Sanda A Adamawa
- Saraki Ya Taya Gwamnonin Da Suka Yi Nasara A Kotun Koli Murna
Ya ce, “Wani bangare da nake sa ran shugaban kasa zai yi jawabi a kai shi ne yawan wadanda aka nada mukaman siyasa. Wasu daga cikin wadanda aka bai wa mukaman ba a bukatan su. Ya kamata gwamnati ta fito da karancin adadin masu mukami ko kuma ta takaita.”
Shekarau yay aba wa Shugaba Tinubu kan dakatar da ministan harkokin jin kai da yaki da fatara, Betta Edu bisa zargin da aka yi mata na badakalan miliyoyin kudade.
Idan za a iya tunawa dai a ranar Litinin ne Shugaban kasa Tinubu ya umurci shugaban hukumar cin hanci da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede da ya binciki dukkan kudaden ma’aikatan jin kai.
Edu ta fuskanci tuhuma ne bayan fallasa wata takarda da aka yi a ranar 20 ga watan Disambar 2023, wacce ta bayyana cewa ta umurci Akanta Janar na tarayya, Oluwatoyin Madein ta tura naira miliyan 585 zuwa wani asusun Oniyelu Bridget, wanda ma’aikatar ta yi ikirarin cewa a yanzu haka tana aiki a matsayin babban akanta na kamfanin “Grants for Vulnerable Groups.”