Kevin de Bruyne ya samu bikin bankwana mai ban sha’awa a filin wasa na Etihad a karo na karshe a daren ranar Talata, kuma a lokacin ne koci Pep Guardiola ya zubar da hawaye, inda kuma ya kira ranar da “ranar bakin ciki”, dan wasan mai shekaru 33 zai tashi a matsayin gwarzon dan wasan Manchester City, kuma ya bayyana cewa “zai kasance a koyaushe” yana goyon bayan City, kungiyar ta bayar da sanarwar cewa za a gina mutum-mutumi, don girmama shi a wajen filin wasansu.
De Bruyne ya fada a cikin jawabinsa na bayan wasan “Kowa ya san yadda nike matukar sha’awar wannan kungiyar kuma zamana a nan ya zama mafi kyawun shekarun rayuwata ta kwallon kafa, abin alfahari ne in yi wasa da wadannan mutanen, na yi abokai da yawa a nan kuma City za ta ci gaba da kasancewa kamar gida a wurina”.
- An Gano Kofin Gasar Zakarun Turai Na Mata Bayan Sace Shi Da Aka Yi
- Tawagar MDD Da Majalisar Shugabancin Libya Sun Kafa Kwamitin Tsagaita Bude Wuta
A tsawon shekaru goma da De Bruyne ya kwashe a Manchester City ta samu nasarorin da ba ta taba samu ba a tarihinta, kuma ta kafa tarihin zamowa kungiya ta farko da ta lashe kofin gasar Firimiya sau hudu a jere, dan wasan ya shiga cikin kundin tarihin kulob din ta hanyar lashe kofuna 16.
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce “Kowa ya ga yadda mutanen Manchester City ke da alaka da shi da danginsa da kuma irin soyayyar da suke nuna mashi, amma kuma wannan rana ce ta bakin ciki kuma za a yi kewarsa, ko shakka babu.”
Guardiola ya kara da cewa “Lokacin da Kebin ya zo nan, na tabbata ba mai goyon bayan Man City ba ne, ban san kungiyar da yake goyon baya ba, amma na tabbata cewa shi mai goyon baya ne a yanzu kuma zai kasance ya na goyon bayanta har abada”.
City ta ba da sanarwa a gabanin fafatawar cewa ta shirya wani babban kyalle mai dauke da sunansa tare da sanya wa wata hanya sunan De Bruyne a makarantar horarwa ta kungiyar, Guardiola yana girmama De Bruyne sosai har ya bayyana dan kasar Belgium din a matsayin dan wasan da ya fi iya kwallo a cikin ‘yan wasan da ya taba horarwa bayan Lionel Messi.
De Bruyne ya fara buga wa City wasa a watan Satumban shekarar 2015, De Bruyne ya buga wasanni 283 a matakin farko, ya ci kwallaye 72 sannan ya taimaka aka zura kwallaye 119 wanda hakan ya sa ya zama na biyu a jerin wadanda suka fi kowa taimakawa wajen zura kwallo a gasar Firimiya bayan Ryan Giggs da yake da 162.
Wasan da suka yi da Bournemouth shi ne wasa na 142 kuma na karshe da De Bruyne ya buga wa City a gida, inda Dabid Silba mai wasanni 160 ne kadai dan wasan da ya fi shi buga wasannin Manchester City na Firimiya Lig a Etihad.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp