Ɗan wasan da yafi kowane dan wasa jefawa kasar Ingila kwallo a tarihi, Harry Kane ya koma Bayern daga Tottenham a watan Agustan 2023 kuma yanzu ya ci kwallaye 58 a wasanni 57 na Bundesliga, Kane ya na da shekaru 31 a duniya, don haka lokaci ya gabato masa a yunkurinsa na kawo karshen jiransa na daukar kofi.
Shekaru goma sha uku a Tottenham amma Ba’ingilen bai samu ya lashe wani kofi ba, hakazalika ya buga kaka guda a Bayern Munich amma duk da hakan ya kasa lashe gasar Bundesliga duk da cewar sun shafe shekaru 8 a jere su na daukar kofin.
- Bayan Hukuncin ‘Yansanda, Sarki Sanusi II Ya Soke Hawan Sallah
- Ko Raunin ‘Yan Wasa Zai Rage Wa Barcelona Karsashi A Kakar Bana?
Amma kuma a wannan kakar ya na kan hanyar lashe kofi ko da guda ne duba da cewar yanzu haka ta na jan ragamar gasar Bundesliga, maki shida tsakaninta da Bayern Leverkusen dake matsayi na biyu, kuma ta na matakin na ku da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai, Bayern dai ta bai wa Bayer Leverkusen tazarar maki shida a teburin gasar saura wasanni bakwai.
Idan kungiyar da Vincent Kompany ke jagoranta ta yi nasara a wasanta da Heidenheim na gaba zai kara tabbatar da su akan turbar lashe Bundesliga, a hakikanin gaskiya Kane zai iya kawo karshen kakar wasa ta bana da kofuna biyu, domin Bayern ta na matakin daf da karshe a gasar zakarun Turai, inda za ta kara da Inter Milan.
Idan Bayern ta lashe kofi a kakar wasa ta bana hakan na nufin Kane zai kasance cikin farin cikin lashe kofi a karon farko a tsawon rayuwar kwallonshi ta shekara 15, Kane ya bugawa kasar Ingila wasanni 105 ya jefa kwallaye 71, a matakin kungiya kuma ya buga wasanni 430 inda ya jefa kwallaye 285.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp